Ashura: 'Yan Shi'a Sun Sanya Ranar da Za Su Gudanar da Tattaki a Fadin Najeriya

Ashura: 'Yan Shi'a Sun Sanya Ranar da Za Su Gudanar da Tattaki a Fadin Najeriya

  • Kungiyar IMN ta 'Yan Shi’a karkashin jagorancin Sheikh Ibraheem Zakzaky ta sanar da gudanar da jerin tattakin Ashura a fadin Najeriya
  • Kungiyar ta ce za a gudanar da jerin gwanon a garuruwa da kauyuka sama da 600 a jihohi fiye da 23 da Abuja a ranar Juma'a
  • Ta bayyana Ashura a matsayin lokacin tunawa da shahadar Imam Husain tare da nuna muhimmancin adalci, gaskiya a rayuwar Musulmi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kaduna - Kungiyar IMN, wadda aka fi sani da kungiyar 'Yan Shi’a karkashin jagorancin Sheikh Ibraheem Zakzaky, ta sanar da shirye-shiryen gudanar da tattakin Ashura a fadin Najeriya.

Kungiyar ta ce za a gudanar da jerin gwanon ne ranar Juma’a, 26 ga Yuni, 2026, domin tunawa da shahadar Imam Husain, jikan Annabi Muhammad (SAW).

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Gwamnatin Tinubu ta kawo shaidu 30 da za su ba da shaida a kotu

'Yan Shi'a za su gudanar da tattakin Ashura a Najeriya
Wasu 'Yan Shi'a mata na gudanar da tattaki a Abuja. Hoto: PHILIP OJISUA/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Shi'a za su gudanar da tattaki

Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa mabiya akidar Shi’a na gudanar da ibada da taruka na musamman a watan Muharram a duk ranakun Ashura.

A cewar kungiyar, tattakin zai gudana a garuruwa da kauyuka sama da 600 da ke cikin jihohi fiye da 23 na Najeriya, har da Babban Birnin Tarayya Abuja.

Kungiyar ta bayyana cewa mabiya ta sun shafe kwanaki suna gudanar da ayyukan tunawa da watan Muharram tun bayan fara sabuwar shekarar Musulunci.

A cikin wata sanarwa da dandalin yada labarai na kungiyar ya fitar tare da sanya hannun Ammar Muhammad-Rajab, an bayyana Ashura a matsayin alama ta tsayin daka wajen adawa da zalunci da kuma kare gaskiya da adalci.

Kungiyar ta ce an dage tattakin zuwa ranar Juma’a, wadda ta yi daidai da 11 ga Muharram, 1448 AH, domin ya yi daidai da bukukuwan tunawa da ake gudanarwa a birnin Karbala da ke kasar Iraki.

Kara karanta wannan

Ana zargin mayakan Turji suna karbar horaswar manya da sababbin makamai

Ashura: Tunawa da adalci da sadaukarwa

Kungiyar ta bayyana cewa duk da cewa za a gudanar da tattakin ranar Juma’a, ayyukan ibadar Ashura za su gudana ranar Alhamis, wato ranar 10 ga Muharram.

Ta ce abin da ya faru a Karbala yana daga cikin muhimman abubuwan tarihi a Musulunci, inda ta ce sadaukarwar Imam Husain na ci gaba da karfafa gwiwar mutane wajen tsayawa kan gaskiya da adalci.

Kungiyar ta ce shahadar Imam Husain ta zama shaida kan nasarar gaskiya a kan karya, adalci a kan zalunci, da kuma tsayin daka wajen kare manufofin da suka dace, in ji rahoton Nigerian Eye.

'Yan Shi'a sun ce za su gudanar da tattakin a fiye da garuruwa 600.
'Yan Shi'a na gudanar da tattaki a Abuja. Hoto: AMINU ABUBAKAR/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Kungiyar ta bayyana manufar tattakin

Kungiyar IMN ta ce tattakin Ashura ba wai lokacin makoki kadai ba ne, har ila yau yana tunatar da jama’a muhimmancin jajircewa wajen fuskantar zalunci da kare gaskiya.

Ta bayyana cewa tattakin na nuna goyon baya da biyayya ga Imam Husain a matsayinsa na mai wakiltar gaskiya da adalci, tare da nuna adawa da duk wani nau’in zalunci.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin jihar Ekiti daga 1999 zuwa yau yayin da ake shirin sabon zabe a 2026

Kungiyar ta kara da cewa za ta ci gaba da gudanar da bikin Ashura a Najeriya a matsayin wani bangare na ayyukanta na tunawa da tarihi da kuma fadakar da mabiyanta kan muhimmancin adalci.

'Yan Shi'a sun yi zanga zanga a Najeriya

A wani labari, mun ruwaito cewa, kungiyar ‘yan Shi’a, karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ta gudanar da zanga-zanga a wasu sassan Najeriya.

Sun yi zanga-zangar ne a jihohin Gombe, Neja, Kano, Bauchi, Yobe da Sakkwato kan kisan Jagoran addinin Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Sun bayyana cewa zanga-zangar ta biyo bayan wani harin sama da aka ce hadin gwiwar Amurka da Isra’ila ne suka kai a Iran, wanda ya janyo mutuwar Khamenei.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com