Bayan Uba Sani, Kotun Ɗaukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Wani Gwamnan APC

Bayan Uba Sani, Kotun Ɗaukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Wani Gwamnan APC

  • Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya samu nasarar a karar da PDP da ɗan takararta suka kai kotun ɗaukaka ƙara
  • Kotun ta kori karar bisa rashin cancanta kana ta tabbatar da nasarar gwamnan na APC a zaben 18 ga watan Maris, 2023
  • Gwamna Abiodun ya yaba da hukuncin yana mai cewa gwamnatinsa zata kara dagewa wajen bunkasa tattalin arzikin Ogun

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a jihar Legas ta yanke hukunci a shari'ar zaben gwamnan jihar Ogun da aka yi ranar 18 ga watan Maris, 2023.

A zaman ranar Jumu'a, 24 ga watan Nuwamba, 2023, kotun ta tabbatar da nasarar Prince Dapo Abiodun na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya ci zaɓen gwamnan Ogun.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta raba gardama, ta yanke hukunci kan nasarar gwamnan APC

Gwamnan jihar Ondo na APC, Dapo Abiodun.
APC ta yi nasara, Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Abiodin Na Ogun Hoto: Dapo Abiodun
Asali: UGC

A mafi rinjayen hukuncin da mai shari'a Joseph Shagbaor Ikyegh ya karanto, ya kori ƙarar da PDP da ɗan takararta, Ladi Adebutu, suka ɗaukaka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma a hukuncin da ɗaya daga cikin alkalan, mai shari'a, Jane Esienanwan Inyang, ya yanke, ya amince da karar, kana ya umarci INEC ta sake sabon zaɓe cikin watanni uku.

Gwamnan ya yi maraba da hukuncin

Sai dai da yake martani kan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara a shafinsa na manhajar X, Gwamna Abiodun, ya yi maraba da hukuncin.

Gwamnan ya bayyana cewa tuni ya shirya tsaf tare da jajircewa wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar da kuma inganta walwalar al'imma.

A kalaman da ya wallafa a shafinsa, Abiodun ya ce:

"Ya ku ’yan kasa kuma mazauna jihar Ogun, ina yi wa jama’a fatan alheri da mika godiyata bisa irin goyon bayan da kuke ba mu a tsawon wannan lokaci."

Kara karanta wannan

Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan nasarar Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna

"Nasarar da muka samu a kotun daukaka kara a yau ba tabbatar da sahihancin amanar da kuka ba mu a zaɓe kaɗai ta yi ba, tana ƙara nuna karfin hadin kan mu."
"Gwamnatinmu zata ƙara zage dantse wajen kawo ci gaba da bunƙasa tattalin arzikin Ogun, ba zamu gajiya ba wajen inganta rayuwar al'umma da ma'aikata."

Kotun ɗaukaka kara ta tabbatar nasarar Gwamna Uba Sani

A wani rahoton kuma Kotun ɗaukaka kara ta kori karar PDP da Isah Ashiru, ta tabbatar da nasarar Malam Uba Sani a zaben gwamnan Kaduna.

Yayin yanke hukunci ranar Jumu'a, kotun mai zama a Abuja ta warware korafi biyar da masu karar suka gabatar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel