Yan Majalisar Dokoki Sun Shirya Zama, Zasu Dora Mataimaki a Matsayin Gwamnan Jihar APC

Yan Majalisar Dokoki Sun Shirya Zama, Zasu Dora Mataimaki a Matsayin Gwamnan Jihar APC

  • Majalisar dokokin jihar Ondo ta kira zama na musamman ranar Jumu'a, 24 ga watan Nuwamba, 2023 kan rikicin siyasar jihar
  • Rahoto ya nuna mai yiwuwa yan majalisar su ayyana mataimakin gwamna, Lucky Aiyedatiwa, a matsayin muƙaddashin gwamna
  • Suna shirin ɗaukar wannan mataki ne duba da halin da Gwamna Rotimi Akeredolu ke ciki tun bayan dawowa jinya daga Jamus

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Mambobin majalisar dokokin jihar Ondo sun shirya zama yau Jumu'a, 24 ga watan Nuwamba, 2023 domin tattauna sarƙaƙiyar siyasar jihar.

Aiyedatiwa tare da gwamna Akeredolu.
Majalisar Dokokin Jihar Ondo Sun Shirya Zama, Da Yiwuwar Sauke Gwamna Hoto: Rotimi Akeredolu, Rotimi Akeredolu
Asali: Twitter

An tattaro daga majiya mai tushe cewa ƴan majalisar dokokin zasu fi maida hankali ne kan ɓangaren masu zartarwa na gwamnatin jihar Ondo karkashin gwamna Rotimi Akeredilu.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Yan bindiga sun buɗe wuta, sun yi garkuwa da shugaban APC a jihar arewa

Matakin da majalisar ke shirin ɗauka

Bayanai sun nuna akwai yiwuwar ƴan majalisar zasu jingine gwamnan gefe guda, su ayyana mataimakin gwamna, Lucky Aiyedatiwa, a matsayin muƙaddashin gwamna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Punch ta ce hakan ya biyo bayan gazawar Gwamna Rotimi Akeredolu na komawa ofis tun bayan dawowa daga kasar Jamus sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita.

Har yanzu Gwamnan na jam'iyyar APC na ci gaba da murmurewa a gidansa na kai da kai da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Amma wata majiya ta bayyana cewa wasu daga cikin yan majalisar ba zasu halarci zaman yau ba saboda saɓanin da ya shiga tsakaninsu kan batun Aiyedatiwa.

Uwar jam'iyya ta ƙasa na goyon bayan zaman

Majiyar, wanda ya nemi a sakaya bayanansa, ya ce zaman da majalisar zata yi yau Jumu'a ya samu cikakken goyon bayan sakateriyar APC ta ƙasa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya shiga tsakani yayin da yan majalisa suka fara shirin tsige gwamnan APC

"Yan majalisa sun shirya zama yau kuma ɗaya daga cikin ajendojin da zasu tattauna ita ce ayyana Lucky Aiyedatiwa a matsayin muƙaddashin gwamna."
"Duk da wasu ƴan majalisa ba zasu halarta ba saboda ba su goyon bayan Aiyedatiwa ya zama gwamnan riko amma APC ta ƙasa ta san da zaman kuma ta amince," in ji shi.

Yayin da aka tuntubi ɗaya daga cikinsu kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar jihar Ondo, Olatunji Oshati, ya tabbatar da batun zaman da suka tsara yau.

Sai dai ya gaza tabbatar da cewa sun tsara ayyana mataimakin gwamna a matsayin muƙaddashin gwamnan jihar Ondo, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Shugaban PDP na Ribas ya yi murabus

A wani rahoton na daban Awanni bayan Bola Tinubu ya naɗa shi a babban muƙami, shugaban APC na jihar Ribas, Desmond Akawor, ya yi murabus.

A wata takarda da ya aike wa shugaban PDP na ƙasa, Akawor, ya ce ya ɗauki matakin ne bayan neman shawari daga jagorori da iyalansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262