Ganduje Ya Saka Labule da Tsohon Shugaban Kasa a Gidansa da Ke Abuja, Bayanai Sun Fito

Ganduje Ya Saka Labule da Tsohon Shugaban Kasa a Gidansa da Ke Abuja, Bayanai Sun Fito

  • Shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Ganduje ya saka labule da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a gidansa da ke Abuja
  • Jam'iyyar APC ce ta sanar da haka da safiyar yau Juma'a 24 ga watan Nuwamba a shafinta na Twitter
  • Sai dai har yanzu ba a san makasudin wannan ziyara ba ta tsohon shugaban kasar yayin da APC ke cin nasara a kotunan zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Dakta Goodluck Jonathan ya ziyarci shugaban APC, Abdullahi Ganduje a gidansa da ke Abuja.

Jam'iyyar APC mai mulki ita ta bayyana haka a shafin Twitter a yau Juma'a 24 ga watan Nuwamba, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Daraktan kamfen PDP ya yi murna bayan shan kaye da PDP ta yi a kotu? gaskiya ta fito

Tsohon shugaban kasa ya ziyarci shugaban jam'iyyar APC, Ganduje
Tsohon shugaban kasa, Jonathan ya kawo ziyara ga shugaban APC, Ganduje. Hoto: APC Nigeria.
Asali: Twitter

Mene dalilin ziyarar Jonathan ga Ganduje?

Sai dai har yanzu ba a san makasudin wannan ziyara ba ta tsohon shugaban kasar zuwa ga shugaban jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

"Shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Ganduje ya karbi bakwancin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a gidansa da ke Abuja."

A kwanakin nan an yi ta cece-kuce Kan hukunce-hukuncen kotuna inda jami'yyar APC ke samun nasara.

Mene martanin gwamnonin PDP da Atiku?

Wannan ziyarar na zuwa ne bayan gwamnonin PDP sun nuna kwarin gwiwarsu a bangaren shari'a.

A taron da su ka gabatar a jiya Alhamis 23 ga watan Nuwamba, gwamnonin PDP sun bayyana kwarin gwiwarsu kan kotun koli yayin da za ta yanke hukuncin karshe.

Sai dai a bangarenshi, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya zargi APC da sauya hukuncin kotuna don bai wa kansu nasara.

Kara karanta wannan

Ku bar ganin Ganduje haka; raina kama ne kaga gayya - Jigo a PDP ya ankarar da Kwankwaso

Atiku ya kuma zargi Tinubu da son mayar da kasar tsarin jam'iyya guda daya wato jami'yyar APC mai mulki.

Kotu ta yanke hukunci kan shari'ar zaben Nasarawa

A wani labarin, Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Nasarawa.

Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa a jiya Alhamis 23 ga watan Nuwamba.

Kotun ta kuma yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, David Ombugadu saboda rashin gamsassun hujjoji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel