Kotun Daukaka Kara Ta Raba Gardama, Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamnan APC

Kotun Daukaka Kara Ta Raba Gardama, Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamnan APC

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci a shari'ar zaben gwamnan jihar Ebonyi da ke Kudu maso Gabashin Najeriya
  • A zaman yanke hukuncin ranar Jumu'a, kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Francis Nwifuru a zaben ranar 18 ga watan Maris, 2023
  • Ta kuma warware korafe-korafen PDP da ɗan takararta kana ta kori karar gaba ɗaya bisa rashin cancanta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ebonyi - Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a jihar Legas, ranar Jumu'a, ta tabbatar da nasarar Gwamna Fran­cis Nwifuru na jihar Ebonyi, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Gwamnan jihar Ebonyi, Fran­cis Nwifuru.
Kotun ɗaukaka kara ta tabbatar da nasarar Gwamnan jihar Ebonyi Hoto: Fran­cis Nwifuru
Asali: Facebook

Kwamitin alkalai uku na Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Jummai Sankey, ne suka yanke wannan hukunci da murya ɗaya ranar Jumu'a, 24 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Bayan Uba Sani, Kotun ɗaukaka kara ta yanke hukunci kan nasarar wani gwamnan APC

Alkalan sun kori ƙarar da Chukwuma Odii, da jam'iyyarsa ta PDP suka ɗaukaka kana suka tabbatar da nasarar Gwamna Nwifuru na jam'iyyar APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ɗaukaka ƙarar ta warware duk batutuwan da ɓangaren masu shigar da ƙara suka gabatar kana daga ƙarshe ta kori ƙarar gaba ɗaya bisa rashin cancanta.

Yayin karanto hukuncin, mai shari'a Sankey ta yi bayanin cewa PDP da ɗan takararta ba su da hurumi a doka na tsoma baki kan harkokin cikin gida na APC.

A cewarta, masu shigar da kara ba su da ikon katsalandan a harkokin APC na cikin gida domin ƙorafin da suka gabatar yana da alaƙa da batun tsaida yan takara.

Nwifuru, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya samu kuri’u 199,131 inda ya doke Ifeanyi Odii na PDP, wanda ya samu kuri’u 80,191.

Kara karanta wannan

Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan nasarar Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna

Bernard Odoh, dan takarar jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), ya zo na uku da kuri'u 52,189 a zaben gwamnan da aka yi ranar 18 ga Maris, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Tinubu Ya Shiga Ganawar Sirri da Dattawan Ondo

A wani rahoton na daban Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tsoma baki a rikicin Gwamna Rotimi Akeredolu, da mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa.

A yanzu haka Tinubu na ganawar sirri da wasu masu ruwa da tsaki daga jihar Ondo yayin da suke neman mafita mai dorewa kan rikicin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel