To Fa: Manyan Jiga-Jigai Sun Matsa a Sauke Gwamnan APC a Ɗora Mataimakinsa a Matsayin Gwamna

To Fa: Manyan Jiga-Jigai Sun Matsa a Sauke Gwamnan APC a Ɗora Mataimakinsa a Matsayin Gwamna

  • Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Ondo sun jaddada buƙatar a baiwa mataimakin gwamna karfin muƙaddashin gwamna
  • A cewarsu, tsawon lokacin da aka ɗauka ba tare da Gwamna Akeredolu ya koma ofis ba ya kara kara ruguza tattalin arziƙin jihar
  • Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Bola Tinubu ya bukaci kowane ɓangare ya sassauta kowa ya tsaya a matsayinsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Wasu manyan jiga-jigai da kusoshin jam'iyyar APC a jihar Ondo sun jaddada cewa ya kamata a ɗora mataimakin gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa, a kujerar muƙaddashin gwamna.

Mataimakin gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa.
Jiga-Jigan APC Sun Jaddada Bukatar Dora Aiyedatiwa a Matsayin Mukaddashin Gwamna Hoto: Lucky Aiyedatiwa
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, jagororin APC sun bukaci a ayyana Mista Aiyedatiwa a matsayin muƙaddashin gwamnan Ondo kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Kara karanta wannan

Ganduje ya kinkimo babban aiki a APC, ya fara shirin kwace wata jiha 1 daga hannun PDP

Idan baku manta ba, shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga tsakani da nufin kawo karshen rikicin siyasar da ya barke tsakanin gwamna da mataimaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Juma’a, Shugaba Bola Tinubu ya nemi kowane ɓangare ya maida wuƙarsa kube kuma Aiyedatiwa ya koma ofishinsa a matsayin mataimakin gwamna, in ji rahoton Leadership.

Amma masu ruwa da tsakin APC na Ondo, a wani taro da suka yi a Akure, sun ce dagon lokacin da aka ɗauka ba tare da Gwamna Oluwarotimi Akeredolu ya koma Ofis ba ya gurgunta tattalin arzikin jihar.

Wace matsaya kusoshin APC suka cimma a taron?

A wata sanarwa da suka fitar bayan taron mai ɗauke da sa hannun shugaba, Afe Olowookere, da sakatare, Raman Rotimi, masu ruwa da tsakin sun aike da saƙo ga majalisar dokoki.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya gana da Ganduje da gwamnoni uku, ya musu nasihar yadda zasu ɗauki talakawa

Sun nemi majalisar ta ayyana mataimakin gwamna, Aiyedatiwa a matsayin muƙaddashin gwamna kafin gwamnan ya gama warkewa.

Sun kuma yanke shawarin cewa ya kamata uwar jam'iyyar APC ta ƙasa ta ƙara zage dantse wajen jan kowa a jiki da mutunta kowa.

Wani sashin sanarwan ya ce:

"Bisa haka ya kamata a riƙa baiwa mambobin jam'iyyar APC dama wajen zaɓen waɗanda zasu rike muƙaman siyasa da na cikin jam'iyya."

Jiga-jigan NNPP na fuskantar barazana

A wani rahoton kuma Jam'iyyar NNPP ta bankaɗo wani rahoto na barazanar da ake yi wa jiga-jiganta da nufin ganin bayansu.

A wasiƙar da ta aike ga IGP, NNPP ta ce wasu da ake wa laƙabi da yan bindigan da ba'a sani ba na shirin kai hari sakateriyar jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel