Akwai Matsala: Yan Majalisa 27 Cikin 31 Sun Juya Wa Gwamnan PDP Baya Yayin da Ake Yunkurin Tsige Shi

Akwai Matsala: Yan Majalisa 27 Cikin 31 Sun Juya Wa Gwamnan PDP Baya Yayin da Ake Yunkurin Tsige Shi

  • Nyesom Wike ya yi ikirarin cewa mambobi 27 daga cikin 31 na majalisar dokokin jihar Ribas ba su tare da Gwamna Siminalayi Fubara
  • Mista Wike, ministan birnin tarayya Abuja ya bayyana haka ne a wata hira ranar Jumu'a kan danbarwar siyasar jihar Ribas
  • Rikicin siyasa ya ɓalle a jihar Ribas tun lokacin da yan majalisa suka yi yunkurin tsige Gwamna Fubara a ƙarshen watan Oktoba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ga dukkan alamu har yanzu akwai sauran rina a kaba a rikicin da ya shiga tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas da magabacinsa, Nyesom Wike.

Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Yan Majalisa 27 Cikin 31 Ba Su Goyon Bayan Gwamna Fubara Na Ribas, In Ji Wike Hoto: Nyesom Wike
Asali: UGC

Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja ya ce yan majalisa 27 cikin 31 na majalisar dokokin jihar Ribas sun sa ƙafar wando ɗaya da Gwamna Fubara.

Kara karanta wannan

Wike ya caccaki Gwamna Fubara, ya bayyana wani laifi 1 da ya yi daga hawansa mulki

Yadda rikici ya raba majalisa gida biyu

Premium Times ta tattaro cewa jihar Ribas ta wayi gari cikin rigingimun siyasa biyo bayan yunkurun wasu ƴan majalisar jihar na tsige Fubara daga kujerar gwamna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan yunƙuri dai shi ne ya haddasa ƙona wasi sashi na zauren majalisar dokokin jihar a ƙarshe-ƙarshen watan Oktoban da ya gabata.

Tun wannan lokaci dai majalisar dokokin ta dare gida biyu, tsagi ɗaya na goyon bayan Wike yayin da ɗayan tsagin kuma na goyon bayan Gwamna Fubara.

Mafi akasarin yan majalisa ba su tare da Fubara

Da yake hira da ƴan jarida kan rikicin siyasar jihar Ribas a Abuja ranar Jumu'a, Mista Wike ya ƙara zafi kan batun Fubara, yana mai cewa shirin tsige shi bai ƙare ba.

“A kowane hali ka tsinci kanka ka gode wa Allah. Babu wani dan siyasa nagari da zai goyi bayan irin haka amma muka yi shiru, na umarci kowa ya kama bakinsa ya yi shiru."

Kara karanta wannan

Wike: Yadda Gwamnan Ribas Ya Tura a Kona Majalisar Dokoki Domin Hana a Tsige Shi

"Bari in tuna maka, kana da mambobi 31 a Majalisar Dokoki, 27 suna adawa da kai" in ji Mista Wike, yayin da yake magana kan Gwamna Fubara.

A hirar wadda TVC News ta watsa, Ministan Abuja ya yi bayani kan rigimar jihar Ribas ciki harda zargin da ake masa na huro wuta da nufin tsige gwamna mai ci.

Da aka tambaye shi ko yana da hannu a tsige magajinsa, Wike ya amsa da cewa, “Idan suna shirin tsige ka,” yana mai nuni ga magajinsa Fubara, “shin ka kira ni?”

Mista Wike ya ci gaba da cewa: "Alal misali mu ɗauka ni ne na shirya makarkashiyar tsige ka, shin ka kira ni ka ce, 'Yallabai suna so su tsige ni."

Shugaba Tinubu Ya Gana da Ganduje da Gwamnoni Uku

A wani rahoton na daban Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnan Kogi, zababbun gwamnonin jihohin Imo da Kogi tare da shugaban APC na ƙasa

Shugaban ƙasan ya taya su murna, yana mai tuna musu cewa su zama bayi masu yi wa al'umma hidima da gyara jihohinsu

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel