Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamna Uba Sani Na Jihar Kaduna

Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamna Uba Sani Na Jihar Kaduna

  • Kotun ɗaukaka kara ta kori karar PDP da Isah Ashiru, ta tabbatar da nasarar Malam Uba Sani a zaben gwamnan Kaduna
  • Yayin yanke hukunci ranar Jumu'a, kotun mai zama a Abuja ta warware korafi biyar da masu karar suka gabatar
  • Sanata Uba Sani ya samu nasarar lashe zaɓen gwamnan Kaduna da aka yi a ranar 18 ga watan Maris, 2023 da tazarar kuri'a sama da 10,000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a birnin tarayya Abuja ta tabbatar nasarar Gwamna Malama Uba Sani na jihar Kaduna.

Kwamitin alƙalai uku na Kotun a ranar Jumu'a sun yanke cewa ƙarar da jam'iyyar PDP da ɗan takararta, Isa Ashiru Kudan suka ɗaukaka ba ta cancanta ba kwata-kwata.

Kara karanta wannan

Bayan Uba Sani, Kotun ɗaukaka kara ta yanke hukunci kan nasarar wani gwamnan APC

Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani.
Kotun ɗaukaka kara ta tabbatar nasarar Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna Hoto: Uba Sani
Asali: Facebook

Kotun ɗaukaka ƙaran ta warware dukkan korafe-korafe biyar da masu ƙara suka gabatar kuma ta wanke Gwamna Uba Sani, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar kotun, babbar shaidar da PDP ta gabatar ya bada bayanin ƙanzon kurege ne kawai domin ba ya nan a lokacin aka yi aringizon kuri'u a zaɓe.

Kotun daukaka kara ta ce zarge-zargen rage kuri’u, cushen akwatunan zabe, da kuma lalata wasu muhimman kayan zabe da shaidan ya yi, duk labari kawai ya ji.

Ta kuma ta kara da cewa kotun zaɓe ta yi daidai da ta kori ƙarar PDD da takararta saboda sun bar shari'ar, daga ƙarshe ta tabbatar da nasarar Uba Sani, rahoton Channels tv.

Yadda shari'ar ta faro a kotun zaɓe

Idan baku manta ba, ɗan takarar gwamna a inuwa PDP, Isah Ashiru Kudan, ya ɗaukaka ƙara bayan hukuncin da kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zabe ta yanke.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari'ar gwamnan PDP, ta ba da dalili

Kotun zabe dai ta tabbatar da nasarar Malam Uba Sani na jam'iyyar APC a zaben gwamnan da aka yi ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Dama tun a farko, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ayyana Sanata Sani, ɗan takara a inuwar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri'u 730,002.

Ashiru wanda ya take masa baya ya zo na biyu ya samu ƙuri'u 719,196, tazarar da ke tsakaninsu ta hauwa 10,000.

Kotun ɗaukaka ƙara ta yi hukunci kan zaben gwamnan Ebonyi

A wani rahoton na daban Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a jihar Legas, ranar Jumu'a, ta tabbatar da nasarar Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi.

Kotun ɗaukaka ƙarar ta warware duk batutuwan da ɓangaren masu shigar da ƙara suka gabatar kana daga ƙarshe ta kori ƙarar gaba ɗaya bisa rashin cancanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel