Shari’ar Kano: ’Yan jam’iyyar NNPP sun yi ganganmin addu'o'i duk da gargadin 'yan sanda

Shari’ar Kano: ’Yan jam’iyyar NNPP sun yi ganganmin addu'o'i duk da gargadin 'yan sanda

  • An samu tashin hankali a Kano, yayin da magoya bayan jam'iyyar NNPP suka yi gangamin salloli da addu'o'i duk da gargadin 'yan sanda
  • A yayin da ake wannan hargitsin, wani dan jam'iyyar ya ce dole su gudanar da addu'a da zanga-zangar lumana kan rashin adalcin da ya ce an yi masu
  • Wannan na zuwa ne dai bayan da Kotun Daukaka Kara ta kori Gwamna Abba Kabir Yusuf daga kujerar gwamnan Kano kan rashin shaidar zama dan jam'iyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Tashin hankali a yayin da magoya bayan jam'iyyar NNPP suka yi gangamin salloli da addu'o'i a Dan Agundi da ke jihar Kano, kan hukuncin Kotun Daukaka Kara.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan sanda sun tura gargadi ga jam'iyyun APC, NNPP kan shirin zanga-zanga a jihar

Kotun Daukaka kara a ranar Juma'ar da ta gabata ta kori Gwamna Abba Kabir Yusuf daga kujerar gwamnan Kano, kan rashin hujjarsa ta zama mamba a jam'iyyar NNPP.

Abba Kabir Yusuf/Gwamnan Kano
Wani dan jam'iyyar NPP ya ce suna da ikon yin addu'o'i da zanga-zangar luma kan rashin adalcin da aka yi masu. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Daily Trust ta ruwaito cewa, addu'o'in da aka gudanar a ranar Alhamis, alama ce ta nuna amincewar jama'ar kan hukuncin da kotun ta yanke, lamarin da ya jawo arangamar 'yan jam'iyyar da jami'an tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mene dalilin addu'o'i da zanga-zangar da 'yan NNPP ke yi?

Irin wannan arangamar ta faru a lokacin jami'an 'yan sanda suka yi yunkurin shiga tsakanin, sai abin ya koma kamar famin kurji, Channels TV ta ruwaito.

A yayin da ake wannan hargitsin, wani dan jam'iyyar NNPP da ya bukaci a sakaya sunansa, ya kare kansu kan zanga-zanga da addu'o'in da suke yi.

"Muna da ikon gudanar da addu'o'i da kuma yin zanga-zanga idan an yi mana rashin adalci. Sai dai, karkashin wannan gwamnati mai kama da mulkin soja, 'yan sanda sun farmake mu."

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin da suka yi nasara a Kotun Daukaka Kara kawo yanzu

A cewarsa.

Kwamishinan 'yan sanda ya magantu

A tsaka da wannan lamarin ne, kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano Husaini Gume ya tabbatar da kokarin jami'an tsaro na dakile masu yunkurin karya doka da oda a jihar da ke Arewa maso Yamma.

Duk da wannan gargadin, magoya bayan NNPP sun dage kan yin zanga-zangar lumana, lamarin da kwamishinan ya kira neman tayar da zaune tsaya musamman yadda suke tare hanyar jama'a.

Kotun Daukaka Kakara ta ce an samu kuskure a takardar CTC

A wani labarin, Kotun Daukaka Kara ta magantu kan takarar hukuncin shari'ar gwamnan Kano da ta yanke, wanda wani sashe ya nuna akasin sakamakon hukuncin kotun.

Legit Hausa ta ruwaito maku yadda wani bangare a cikin takardar ya nuna cewa kotun ta tabbatar da nasarar zaben Gwamna Abba Kabir Yusuf, sabanin sanar da korarsa da kotun ta yi a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel