Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Yi Murabus Bayan Bola Tinubu Ya Naɗa Shi a Babban Muƙami

Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Yi Murabus Bayan Bola Tinubu Ya Naɗa Shi a Babban Muƙami

  • Awanni bayan Bola Tinubu ya naɗa shi a babban muƙami, shugaban APC na jihar Ribas, Desmond Akawor, ya yi murabus
  • A wata takarda da ya aike wa shugaban PDP na ƙasa, Akawor, ya ce ya ɗauki matakin ne bayan neman shawari daga jagorori da iyalansa
  • Tun farko, shugaban ƙasa ya naɗa Mista Akawor a matsayin kwamishinan tarayya mai wakiltar Ribas a hukumar RMAFC

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na jihar Ribas, Desmond Akawor, ya yi murabus daga muƙamin, kamar yadda Punch ta tattaro.

Takardar murabus ɗin shugaban PDP ta bayyana ne ranar Jumu'a awanni bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa shi a shirgegen muƙami na tarayya.

Kara karanta wannan

Ana cikin zaman lafiya Ganduje ya tono sabuwar rigima a jam'iyyar APC

Shugaban PDP na jihar Ribas ya yi murabus.
Mutumin da Tinubu Ya Nada a Mukami Ya Yi Murabus Daga Shugaban PDP na Rivers Hoto: Punchng
Asali: UGC

Idan baku manta ba shugaba Tinubu ya naɗa shi a matsayin kwamishinan tarayya mai wakiltar jihar Jihar Ribas a hukumar tattara kuɗin shiga ta kasafi RMAFC, rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A takadar mai ɗauke da kwanan watan 22 ga watan Nuwamba, da adireshin muƙadɗashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagun, Mista Akawor, ya ce ya yi murabus ne sabida mukamin da ya samu.

Ya kuma bayyana cewa ya jima da miƙa ragamar harkokin jam'iyyar PDP ga mataimakinsa, Chukwuemeka.

Meyasa ya ɗauki matakin murabus?

Wani sashin wasiƙar ya ce:

"Kwanan nan aka zabe ni a muƙamin tarayya na Hukumar Tattara Kudaden shiga da ƙasafta su a matsayin Kwamishinan Tarayya mai wakiltar Jihar Ribas."
"Bayan neman shawarwari daga shugabanni da iyalai na, na amince da wannan damar ta yi wa kasarmu hidima, wadda nake gani a matsayin damar bautawa kasa."

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaba Tinubu ya sa labule da gwamnonin APC da PDP a Villa, bayanai sun fito

"Bisa haka na yi murabus daga mukamina na shugaban jam’iyyarmu ta PDP na jihar Ribas, kuma nan take na mika ragama ga mataimakin shugaban jam’iyyar, Aaron Chukwuemeka, wanda ya fara aiki a wannan matsayi."

Daga ƙarshe, ya gode wa jam'iyyar PDP bisa damar da ta ba shi musamman daga shekarar 2020 zuwa 2023, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Mista Akwor ya kuma miƙa godiya ga shugaban ƙasa, Bola Tinubu bisa ganin ya dace kuma ya zaƙulo shi ya naɗa shi wannan muƙami da zai yi wa ƙasa hidima.

Gwamnonin PDP Sun Gana a Abuja

A wani rahoton na daban Gwamnonin PDP sun bayyana kwarin guiwa cewa kotun koli zata yi adalci a hukuncin tsige gwamnonin Zamfara da Filato.

Sun bayyana hukuncin kotun ɗaukaka ƙara a matsayin wani koma baya na wucin gadi ga Dauda Lawal da Caleb Mutfwang.

Asali: Legit.ng

Online view pixel