Siyasar Najeriya
A yau ne za a gudanar da zaben gwamnan jihar Edo da ke Kudu Maso Kudancin Najeriya, zaben dai zai ja hankali musamman a tsakanin ƴan takarar PDP, APC da LP.
Yayin da zabe ya kankama a mafi yawan rumfunan zaɓe, Asur Ighodalo ya bayyana damuwa kan abin da ya kira barazanar tsaro a sassan jihar yau Asabar.
Sabuwar rigima ta barke a wata rumfar zabe da ke karamar hukumar Orhionmwon ta jihar Edo a ranar Asabar bayan da jami'an INEC suka manta da takardar rubuta sakamako.
Dan majalisar wakilan tarayya daga jihar Benuwai, Hon. Terseer Ugbor ya yi barazanar maka Gwamna Alia da gwamnatinsa a kotun kan zargin karyar da suka masa.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar NNPP a zaben shugaban kasa na 2023 ya ce jam'iyyar za ta taka rawar gani a zaben 207 yayin da ta dauki matakai tun yanzu.
Gwamnatin Edo karkashin gwamna Godwin Obaseki ta ce wasu miyagu na nan suna yawo a kan tituna da shirin tarwatsa harkokin zaɓe a kananan hukumomin jihar.
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana wasu yan siyasar Najeriya a matsayin barayi inda ya ce ya kamata mafi yawansu suna gidan yari.
Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta yi fatali da karar APP wadda ta nemi a ba da damar maye gurbin ƴan majalisa 27 da suka sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Jagoran siyasar jihar Kano kuma jigon jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sha alwashi kan zaben 2027 inda ya ce suna kan shirin game da haka.
Siyasar Najeriya
Samu kari