Kwankwaso Ya Yi Muhimmin Kira Ga Masu Ruwa da Tsakin Arewa Kan Tinubu

Kwankwaso Ya Yi Muhimmin Kira Ga Masu Ruwa da Tsakin Arewa Kan Tinubu

  • Jigo a jam'iyyar APC kuma tsohon kwamishina a jihar Kano, Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi kira ga jiga-jigan Arewacin Najeriya
  • Kwankwaso ya buƙaci masu ruwa da tsaki na yankin da su marawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ƙoƙarin da yake yi na kai ƙasar nan tudun mun tsira
  • Ya buƙace su da su yi watsi da masu sukar shugaban ƙasan saboda a cewarsa ya goyin bayan Muhammadu Buhari a shekara takwas da ya yi yana mulki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Jigo a jam'iyyar APC Alhaji Iliyasu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki na Arewacin Najeriya su marawa Shugaba Bola Tinubu baya.

Musa Kwankwaso ya buƙace su da suyi watsi da ƴan tsirarun da ke sukar gwamnatin shugaban ƙasan a ƙoƙarin da yake na kai ƙasar nan zuwa tudun mun tsira.

Kara karanta wannan

Matawalle: EFCC ta yi magana kan binciken tsohon gwamnan Zamfara

Kwankwaso ya shawarci 'yan Arewa kan Tinubu
Musa Iliyasu Kwankwaso ya bukaci jiga-jigan Arewa su marawa Tinubu baya Hoto: Musa Iliyasu Kwankwaso, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Wane kira Musa Kwankwaso ya yi?

Jaridar Tribune ta ce Musa Iliyasu Kwankwaso ya jaddada cewa ya kamata jiga-jigan Arewa su goyi bayan Bola Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, Tinubu ya bayar da cikakken goyon baya ga magabacinsa, Muhammadu Buhari, a tsawon shekara takwas da ya yi yana mulki.

'Dan siyasar ya yi Allah-wadai da zanga-zangar da aka yi kan Bello Matawalle, inda ya bayyana ta a matsayin wani ɓangare na ƙulla-ƙullar da ake yi wa Shugaba Tinubu.

Bayan nan ya kara da zargin cewa ana yi wa Abdullahi Umar Ganduje, da sauran jiga-jigan ƴan siyasa na jam’iyya mai mulki bita-da-kulli.

Kwankwaso ya zargi wasu ƴan siyasa da nuna fuska biyu, inda ya caccake su kan rashin sukar Buhari a tsawon shekara takwas da ya yi yana mulki amma a yanzu sun taso Tinubu a gaba.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya fadi dalilin da ya sa gwamnatin Kano ta yi wa Ganduje illa a siyasance

Ya kuma buƙaci dattawan Arewa da su hada kai da gwamnonin yankin domin kawo romon dimokuraɗiyya wanda zai amfani al'ummar yankin.

... Musa Kwankwaso ya shawarci ƴan majalisu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jigon APC a jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya buƙaci ƴan majalisun tarayya da suka fito daga yankin Arewa da su haɗa kansu.

Musa Kwankwaso ya nemi ƴan majalisun da kada su bari rashin jituwa ya shiga tsakaninsu, sakamakon zargin yin cushe a kasafin kuɗin shekarar 2024.

Asali: Legit.ng

Online view pixel