Majalisar Dokokin Ribas Ta Yi wa Gwamnan PDP Barazana, Ta Ammince da Ƙarin Kudiri 1

Majalisar Dokokin Ribas Ta Yi wa Gwamnan PDP Barazana, Ta Ammince da Ƙarin Kudiri 1

  • Majalisar dokokin jihar Ribas ta sake bijirewa Gwamna Siminalayi Fubara a karo na uku cikin watanni uku
  • A zaman ranar Litinin, 6 ga watan Mayu, majalisa ta amince da kudirin sayen kayan gwamnati ya zama doka
  • Ta kuma yi barazanar cewa za ta ɗauki tsattsauran mataki kan Gwamna Fubara idan ya ci gaba da yin watsi da dokokin majalisar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Majalisar dokokin jihar Ribas ta sake tono rikicin siyasar da aka jima ana yi a jihar, inda ta amince da kudirin dokar da Gwamna Siminalayi Fubara ya ƙi sa wa hannu.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, wannan shi ne karo na uku a cikin watanni uku da majalisar dokokin ta bijirewa Gwamna Fubara wajen amincewa da doka.

Kara karanta wannan

"Ban san da zamanku ba", Fubara ya yi kakkausar suka ga 'yan majalisar Rivers

Gwamna Fubara na Ribas.
Majalisar jihar Ribas ta sake nuna karfin doka kan Gwamna Fubara Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Twitter

Sabanin 'yan majalisar Ribas da gwamna Fubara

A watan Maris da ya gabata, majalisar Ribas ta raba gari da Fubara game da batun kafa hukumar kula da harkokin majalisar dokokin jihar Ribas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan ta sake bijirewa gwamnan a watan Afrilu yayin da ƴan majalisar suka kaɗa ƙuri'ar amincewa da kudirin garambawul ga dokar ƙananan hukumomi wanda Fubara ya ƙi sa wa hannu.

A yau Litinin, 6 ga watan Mayu, majalisar ta kuma sake amincewa da kudirin sayen kayan gwamnati 2024 ya zama da doka duk da ƙin amincewar Fubara.

Majalisa ta sake yi wa Mai girma Fubara barazana

Majalisar ta kuma yi barazanar ɗaukar matakai masu tsauri kan gwamnan matuƙar ya ci gaba da sa kafa yana shure dokokin da ta amince da su.

Da yake jawabi kan kudirin da suka bijirewa gwamna, kakakin majalisar Martin Amaewhule, ya ce sun amince da shi ne domin tsare kuɗin harajin da jihar ke tarawa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta musanta shirin korar wadanda Ganduje ya dauka aiki

Ya kuma ƙara da cewa dokar za ta tabbatar da cewa ba a kashe kuɗaɗen a wasu bara gurbin kwangiloli ba, Channels tv ta ruwaito wannan.

Amaewhuleya koka kan yadda aka yi watsi da tsarin baya, aka koma ba da kwangila da ba tare da bin tanadin doka ba kana mulkin jihar ya koma kamar na kama karya.

PDP ta rasa ƙusoshi a Ebonyi

A wani rahoton na daban abubuwa sun kara dagulewa a jam'iyyar PDP yayin da wasu manyan ƙusoshi suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC a Ebonyi.

Sylvanus Ngele, tsohon ɗan majalisar dattawa da ɗan takarar gwamna a zaɓen 2023 na cikin waɗanda suka haƙura da PDP a taron ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel