Ribas: Gwamna Ya Ɗauki Zafi Yayin da APC Ta Umurci Majalisa Ta Tsige Shi Nan Take

Ribas: Gwamna Ya Ɗauki Zafi Yayin da APC Ta Umurci Majalisa Ta Tsige Shi Nan Take

  • Gwamna Simi Fubara ya hana ciyamomi da dukkan jagororin kananan hukumomi 23 bayyana a gaban majalisar dokokin Ribas karkashin Martin Amaewhule
  • Wannan mataki na zuwa ne awanni 24 bayan APC ta umurci majalisar ta fara shirin tsige Fubara daga kujerar gwamna
  • Tun farko dai Fubara ya yi iƙirarin cewa doka ba ta san da zaman ƴan majalisar ba saboda sun sauya sheƙa zuwa APC

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya ɗauki zafi yayin da rikici ya dawo ɗanye tsakaninsa da majalisar dokokin jihar.

Fubara ya sanar da haramtawa dukkan ciyamomi da manyan jami'ai a kananan hukumomin jihar zuwa gaban majalisar musamman mai goyon bayan Nyesom Wike.

Kara karanta wannan

Majalisa ta ɗauki wasu matakai na ƙawo ƙarshen satar ɗalibai da tsaro a Najeriya

Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas.
Fubara ya haramtawa ciyamomi bayyana a gaban majalisar dokokin jihar Ribas Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Twitter

Fubara ya yi barazanar tsige ciyamomi

Gwamnan ya yi barazanar tsige duk wani ciyaman da ya bayyana gaban majalisar dokokin da Martin Amaewhule ke jagoranta, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan umurni da Gwamna Fubara ya bayar na kunshe ne a wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na hukumar ƙananan hukumomin Ribas, Ebirieneuket Nteile C ya fitar.

Sanarwar mai ɗauke da kwanan watam ranar 7 ga watan Mayu, 2024 ta ce:

"An umarci na faɗa maku dukkan manyan jami'an kananan hukumomi 23 cewa ka da wanda ya kuskura ya bayyana a gaban majalisar dokokin jihar nan.
"Ko da kuwa wasu daga ciki ko tawaga sun aiko maku da takardar gayyata kar wanda ya je ba tare da izinin muƙaddashin shugaban hukumar kula da kananan hukumomi ba."
"Duk wani jami'i da ya karya wannan umarni za a kore shi daga aiki nan take, muna fatan za ku ɗauki wannan mataki da nuhimmanci."

Kara karanta wannan

Sojoji sun dauki mataki bayan kwashe kwanaki a kauyen da aka kashe jami'ai

Yadda gwamna Fubara ya tono rikicin Ribas

Wannan umarni na zuwa ne bayan Gwamna Fubara ya ce doka ba ta san da zaman ƴan majalisa 27 ba saboda sun rasa kujerunsu bayan sauya sheƙa zuwa APC.

Haka nan ya ce ya amince da su ne kawai saboda a zauna lafiya amma hatta sulhun da Bola Ahmed Tinubu ya masu ba ya cikin kundin tsarin mulki, PM News ta tattaro.

Wannan maganganu da Fubara ya yi sun harzuƙa jam'iyyar APC kuma ta fito ta umurci majalisar dokoki ta fara shirin tsige shi nan take.

ALGON ta goyi bayan tsige gwamna Fubara

A wani rahoton kuma, an ji kungiyar ƙananan hukumomin (ALGON) reshen jihar Rivers ta zargi Gwamna Fubara da laifin yin bake-bake kan kuɗaɗen su.

ALGON ta hannun shugabanta na jihar, Allwell Ihunda, ta zargi gwamnan da riƙe kuɗaden da aka warewa ƙananan hukumomi 23 na jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel