APC Ta Yi Babban Kamu Bayan Jigon Jam'iyyar Adawa Ya Dawo Cikinta

APC Ta Yi Babban Kamu Bayan Jigon Jam'iyyar Adawa Ya Dawo Cikinta

  • Ɗan takarar majalisar wakilai na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a zaben 2023, Obinna Nwosu ya koma jam’iyyar All Progressives Party (APC)
  • Obinna Nwosu ya koma jam’iyyar APC ne watanni shida bayan ya yi murabus daga jam’iyyar ADC a watan Nuwamban 2023
  • Shugaban jam'iyyar APC na mazaɓarsa, Cif Chikezie Ekwulebe ne ya karɓe shi tare da ba shi katin zama ɗan jam’iyyar mai mulki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Umuahia, jihar Abia - Ɗan takarar majalisar wakilai na jam'iyyar ADC a mazaɓar Ikwuano/ Umuahia a jihar Abia a 2023, Obinna Nwosu, ya koma jam'iyyar APC.

Obinna Nwosu ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar ADC a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba, 2023.

Kara karanta wannan

Sanata, tsohon ɗan majalisa da manyan ƙusoshin PDP sun sauya sheƙa zuwa APC

Obinna Nwosu ya koma APC
Obinna Nwosu ya zama dan jam'iyyar APC a jihar Abia Hoto: Obinna Nwosu
Asali: UGC

A cikin wasiƙar da ya aika ga shugabannin jam’iyyar ADC, Obinna Nwosu ya godewa jam’iyyar bisa damar da ta ba shi na tsayawa takara a ƙarƙashinnta a zaɓen da ya gabata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta yi babban kamu daga ADC

A ranar Laraba, 8 ga watan Mayun 2024, Obinna Nwosu ya yi rajista a matsayin ɗan jam'iyyar APC a mazaɓar Nkwoegwu da ke ƙaramar hukumar Umuahia ta Arewa a jihar Abia.

Shugaban mazaɓar Nkwoegwu, Cif Chikezie Ekwulebe ne ya ba shi katin zama ɗan jam’iyyar APC.

Shugaban jam'iyyar na mazaɓar ya bayyana cewa:

“APC ta yi babbar huɓɓasa ta hanyar nuna ƙarfin da take da shi na iya jawo matasan ƴan siyasa daga jam'iyyun adawa."

Meyasa Obinna Nwosu ya koma Jam'iyyar APC?

Da yake magana kan dalilinsa na komawa APC a X, ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan

Bello Matawalle: APC ta fadi manufar masu son ganin EFCC ta binciki minista

"Na koma jam'iyyar APC ne domin goyon bayan gwamnati da ba da gudunmawa wajen ci gaban ƙasar mu. Ina miƙa godiya ga dukkan magoya baya na waɗanda suka kasance tare da ni a wannan tafiyar."
"Ina fatan wannan sabon babin da na buɗe zai ƙarfafa gwiwar matasan jihar Abia da matasan Igbo su fara haɗa kansu da siyasar ƙasa."

APC ta fara zawarcin gwamna a adawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ya buƙaci gwamnan jihar Abia, Alex Otti, da ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Gwamna Alex Otti ya bar jam’iyyar APC ne kafin zaɓen 2023 a lokacin da ya kasa samun tikitin tsayawa takarar gwamna a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng