Mutum 18 'Yan Asalin Jihar Sakkwato Sun Mutu Lokaci Guda a Hanyar Dawowa daga Legas

Mutum 18 'Yan Asalin Jihar Sakkwato Sun Mutu Lokaci Guda a Hanyar Dawowa daga Legas

  • Mutane 18 'yan asalin Jihar Sakkwago sun mutu a hatsarin mota da ya rutsa d su a titin Yauri da ke Jihar Kebbi
  • Rahotanni sun nuna na cewa mamatan na dawowa ne daga jihar Legas, inda suka je neman abin dogaro da kansu
  • Wani mamban kungiyar direbobi ta NURTW, Bello Muhammad ya ce mutum biyu kadai suka tsira daga cikin mutane 20 da ke cikin motar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kebbi, Nigeria - Akalla mutane 18 'yan aslin jihar Sakkwato sun rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a kan hanyar Yauri da ke Jihar Kebbi.

Sakkwatawan sun gamu da ajalinsu ne yayin da suke dawowa gida daga Legas, inda suka je neman abin dogaro da kai.

Kebbi.
Taswirarjihar Kebbi da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Daily Trust ta ruwaito cewa mamatan na cikin fasinjoji 20 da ke cikin wata motar haya mai kujeru 18 lokacin da ta yi taho-mu-gama da wata tirela da misalin karfe 11:00 na dare ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Yan kwallo sun rasu bayan hadari a Kebbi, gwamna ya ba su miliyoyin Naira

Sakkwatawa 10 sun mutu a hatsari

Lamarin ya yi sanadin mutuwar mutum 18 nan take, yayin da mutum biyu suka tsira da raunuka.

Wani ganau ya shaida cewa fasinjojin sun kwashe wani lokaci a Legas suna neman kuɗi kafin suka kama hanyar komawa gida a Sakkwato.

Wani dan Kungiyar Direbobin Motoci ta Kasa (NURTW), Bello Muhammad, wanda kuma abokin marigayi direban motar ne, ya ce yana cikin wadanda suka taimaka wajen kwashe gawarwakin bayan samun labarin hatsarin.

Ya ce:

"An sanar da mu cewa abokin aikinmu ya yi hatsari a bayan garin Yauri. Da muka isa wurin, mutane 18 sun riga sun mutu, motar kuma ta lalace matuka."

An kwashe gawarwaki zuwa asibiti

Bello Muhammad ya ce an kai gawarwakin zuwa Babban Asibitin Yauri, inda 'yan uwa suka tantance su kafin a mika musu domin jana'iza.

Ya bayyana cewa shi da kansa ya dauki gawarwakin wadanda suka fito daga gundumar Kajiji zuwa garuruwansu domin birne su.

Kara karanta wannan

Abin da gwamnatin Katsina ta ce da aka kama shugabannin ƴan ta'adda a filin jirgi

Ya bayyana wasu daga cikin mamatan da suka hada da direban motar, Manniru Sabo, Basiru Shehu da wani mutum daga daya daga cikin kauyukan gundumar Kajiji.

Jami'an FRSC.
Jami'an hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) sun kai dauki bayan an yi hatsari Hoto: FRSC
Source: Facebook

Ya kuma ce mutum bakwai daga cikin mamatan sun fito ne daga kauyukan Bingaje da Gudirriga a karamar hukumar Yabo, yayin da wasu biyu suka fito daga karamar hukumar Gada.

Muhammad ya ce saboda tsananin lalacewar wasu daga cikin gawarwakin, za a binne su ne a Yauri, yayin da aka kai wadanda aka iya daukowa zuwa Kajiji, inda aka yi musu jana'iza bisa koyarwar addinin Musulunci.

Ya kara da cewa mutum biyu ne kawai suka tsira daga hatsarin, kuma daya daga cikinsu shi ne mai karbar kudin mota, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Hatsari ya rutsa da sojoji da yan NYSC

An ji cewa akalla mutum shida sun mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da sojoji da 'yan bautar kasa a jihar Adamawa.

Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya ya haddasa gobara mai karfi da ta kona motar haya tare da kashe dukkan fasinjojin da ke cikinta.

Binciken farko ya nuna cewa hudu daga cikin wadandaNsuka mutu mambobin hukumar yi wa kasa hidima ta NYSC ne da aka tura aiki a jihar Adamawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262