Edo: Shugaban Majalisa Ya Dakatar da Ƴan Majalisa 3 Na PDP da APC, Bayanai Sun Fito

Edo: Shugaban Majalisa Ya Dakatar da Ƴan Majalisa 3 Na PDP da APC, Bayanai Sun Fito

  • Shugaban majalisar dokokin jihar Edo, Blessing Agbebaku, ya dakatar da ƴan majalisa uku a ranar Litinin, 6 ga watan Mayu, 2024
  • Lamarin dai ya haddasa hayaniya a majalisar yayin da waɗanda aka dakatar suka yi fatali da matakin nan take
  • Sun shaidawa kakakin majalisar cewa bai isa ya dakatar da su shi kaɗai ba dole ya bar sauran mambobi su kaɗa kuri'a

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Kakakin majalisar dokokin jihar Edo, Blessing Agbebaku, na jam'iyyar PDP ya dakatar da ƴan majalisa uku ranar Litinin, 6 ga watan Mayu, 2024.

Rahotanni sun nuna cewa an dakatar da ƴan majalisar ne saboda yunƙurin haifar da fargaba a zauren majalisar ta hanyar amfani da ƴan tsubbu.

Kara karanta wannan

Majalisar dokokin Ribas ta yi wa gwamnan PDP barazana, ta amince da ƙarin kudiri 1

Majalisar dokokin jihar Edo.
Rigima ta kaure a majalisar dokokin Edo bayan dakatar da mambobi 3 Hoto: Rt Hon. Blessing Agbebaku
Asali: Facebook

Haka zalika an ɗauki matakin dakatar da mambobi uku na majalisar ne bisa zargin sun fara kulla makircin tsige kakakin majalisar da wasu jagorori.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakatarwar ta taɓa PDP da APC a majalisa

‘Yan majalisar da aka dakatar sun hada da Donald Okogbe (PDP, Akoko-Edo II), Bright Iyamu (PDP, Orhionmwon II), da Adeh Isibor (APC, Esan ta Arewa maso Gabas I).

Shugaban majalisar dokokin jihar Edo, Honorabu Agbebaku ne ya sanar da dakatar da mambobin 3 a zaman yau Litinin, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Mista Agbebaku ya zargi ƴan majalisar da yunƙurin ta da yamutsi a zauren majalisar da kuma shirin tsige shugabannin majalisa.

Edo: Meyasa aka dakatar da ƴan majalisar?

Kakakin ya kuma bayyana cewa wasu mutane sun kawo bokaye zauren majalisar ranar 1 ga watan Mayu, 2024 kuma sun yi tsubbace-tsubbace kana suka bar layoyi a wurin.

Kara karanta wannan

Sanata, tsohon ɗan majalisa da manyan ƙusoshin PDP sun sauya sheƙa zuwa APC

Sai dai wannan dakatarwa ta kawo yamutsi a zauren majalisar domim nan take ƴan majalisar da matakin ya shafa suka sa ƙafa suka shure dakatarwar.

A cewarsu:

"Mai girma shugaban majalisa, ba ka da damar dakatar da kowane dan majalisar haka kawai, dole ne sai kowane mamba ya kaɗa kuri'a, ka bar mambobi su kaɗa kuri'a."

Domin kawo ƙarshen tada jijiyoyin wuya tsakanin ƴan majalisar, nan take Agbebaku, ya ɗage zaman majalisar, jaridar Vanguard ta ruwaito wannan.

Shettima zai tafi taro a Amurka

A wani labarin, Kashim Shettima zai kama hanya zuwa ƙasar Amurka dominɓhalartar taron kasuwanci ranar Litinin, 6 ga watan Mayu, 2024

Mataimakin shugaban ƙasar zai wakilci Bola Ahmed Tinubu a taron wanda aka shirya gudanarwa a birnin Dallas domin tattauna yadda za a bunƙasa Afirka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel