An Nemi Kotu ta Dakatar da Abdullahi Umar Ganduje Daga Shugabancin APC

An Nemi Kotu ta Dakatar da Abdullahi Umar Ganduje Daga Shugabancin APC

  • Wani jigo a jam’iyyar APC Mohammed Saidu Etsu ya shigar da kara kotu yana kalubalantar Abdulahi Umar Ganduje a matsayin shugaba na kasa
  • Haka kuma ya nemi kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta dakatar da Ganduje daga bayyana kansa da shugaban APC ko jagorantar taron uwar jam'iyyar ta kasa
  • Jigon na APC ya nemi kotu ta tabbatar da cewa kwamitin koli na jam’iyyar ba shi da hurumin nada Dr. Ganduje a matsayin shugabansu da aka yi a watan Agusta

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano - Wani jigo a jam’iyyar APC, Mohammed Saidu Etsu ya shigar da kara kotu yana kalubalantar Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaba.

Kara karanta wannan

Aikin Kwankwaso ne: Lauyan APC ya 'tona' masu neman karya Ganduje a siyasa

Haka kuma ya nemi kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta dakatar da Abdullahi Umar Ganduje daga bayyana kansa a matsayin shugaban APC.

Shugaban APC, Andullahi Umar Ganduje
Wani jigo a APC na neman Kotu ta dakatar da Abdullhi Umar Ganduje daga shugabancin jam'iyyar Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Rigimar Ganduje a APC NWC

Jigon na APC ya nemi kotu ta tabbatar da cewa kwamitin koli na jam’iyyar ba shi da hurumin nada Dr. Abdullahi Ganduje a matsayin shugabansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mohammed Saidu Etsu, wanda ya taba neman takarar shugabancin jam’iyyar ya kai karar Abdullahi Ganduje ta hannun lauyansa J. Obono Obla yana neman a takawa Shugaban birki, kamar yadda Leadership News ta wallafa.

Etsu ya kalubalanci nadin Ganduje

Daya daga jiga-jigan APC Mohammed Saidu Etsu ya kara janyo baraka a jam’iyyar APC yana kalubalantar yadda jam’iyyar ta nada Abdullahi Ganduje shugabancinta.

A ranar 27 ga Agustan 2023 ne aka maye gurbin Abdullahi Adamu da Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaba, kamar yadda The Guardian ta wallafa

Kara karanta wannan

"Zai yi wahala": Lauyan APC ya fadi hanya 1 da Ganduje zai rasa muƙaminsa a jam'iyya

Amma tsohon dan takarar kujerar shugabancin jam'iyyar, Mohammed Saidu Etsu na ganin wannan ya sabawa sashe na 31.5 tsarin jam’iyyar.

Wannan sabuwar dambarwar ta biyo jerin matsaloli irin na siyasa da Ganduje ke fuskanta a kwanakin nan.

Daga cikin dambarwar siyasar akwai kokarin korarsa da shugabannin mazabar Ganduje ke kokarin yi, da tuhumar almundahana da gwamnatin Kano ke yi masa.

Har yanzu kotu ba ta sanya ranar fara sauraren karar ba.

APC: Kotu ta dakatar da korar Ganduje

A baya kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta dakatar da shugabannin jam'iyyar APC a mazabar Ganduje daga korar shugaban jam’iyyar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje har sai an kamala sauraran karar.

Mai Shari'a, A M Liman ne ya yanke hukunci bayan tsagin da ke dake goyon bayan Abdullahi Ganduje ya shigar da kara kan kokarin korarsa da ake yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel