Kotun Koli Ta Yi Hukuncin Karshe, Ta Takawa Trump Birki kan 'Yancin Jarirai
- Kotun koli ta Amurka ta soke umarnin Donald Trump da ke ƙoƙarin takaita bai wa jariran da aka haifa a ƙasar zama 'yan ƙasa
- Alƙalan kotun sun ce kundin tsarin mulkin Amurka ya ba duk wanda aka haifa a ƙasar damar zama ɗan ƙasa, ba tare da la'akari da matsayin iyayensa ba
- Hukuncin ya zama babban koma baya ga Trump, wanda zai buƙaci gyaran kundin tsarin mulki idan har yana son sauya dokar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Kotun koli ta Amurka ta soke umarnin zartarwa da Shugaba Donald Trump ya fitar a kasar.
Kotun ta dakile umarnin ne wanda ke neman takaita bai wa jariran da aka haifa a Amurka zama 'yan ƙasar.

Source: Getty Images
A hukuncin da alƙalai shida suka goyi baya yayin da uku suka yi adawa, kotun ta ce kundin tsarin mulkin Amurka ya tabbatar da zama ɗan ƙasa ga duk wanda aka haifa a ƙasar, cewar Al Jazeera.

Kara karanta wannan
Tsaro: Najeriya na neman agajin kasashe bayan Trump ya ce ya gama kare ran Kiristoci
Kotun ta ce wannan ya haɗa da yaran da iyayensu ba su da takardun zama a Amurka ko kuma suke zaune a ƙasar na ɗan lokaci.
Babban Alƙalin Kotun Koli, John Roberts, ya ce wannan tanadi na zama ɗan ƙasa muhimmin ginshiƙi ne na dimokuraɗiyyar Amurka kuma dole ne a ci gaba da mutunta shi.

Source: Facebook
Ya ce gyara na 14 na kundin tsarin mulkin Amurka ya ba kowane mutum da aka haifa a ƙasar wannan haƙƙi, kuma kotun ta tabbatar da hakan.
Ya ce:
"A da da kuma yanzu, zama ɗan ƙasa na nufin samun haƙƙoƙi da damar cin moriyar waɗannan haƙƙoƙin, ciki har da 'yancin shiga da cikakken 'yanci cikin harkokin siyasar al'umma. Masu tsara gyara na 14 ga Kundin Tsarin Mulki sun faɗaɗa wannan alƙawari ga 'duk wani mutum da aka haifa cikin 'yanci a wannan ƙasa."
Trump dai ya daɗe yana sukar wannan tanadi, yana mai cewa wasu baƙi na zuwa Amurka ne domin haihuwa kawai domin 'ya'yansu su samu zama 'yan ƙasar, cewar rahoton Channels TV.
Sai dai bayan wannan hukunci, umarnin zartarwar Trump ya zama ba shi da wani tasiri a doka, kuma hanya ɗaya da ta rage masa ita ce neman a yi wa kundin tsarin mulki gyara.
Karin bayani na tafe....
Alkalan ICC sun kai Trump kara kotu
Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin Amurka karkashin jagorancin shugaban kasa, Donald Trump, ta kakaba takunkumi kan wasu alkalan kotun ICC.
Alkalan sun koka kan takunkumin da aka sanya masu inda daga karshe suka dauki matakin kai Donald Trump kara gaban kotu.
Takunkumin da aka sanyawa alkalan ya biyo bayan sammacin da kotun ta bayar ne na cafke Firaministan Israila, Benjamin Netanyahu.
Asali: Legit.ng
