Bello Matawalle: APC Ta Fadi Manufar Masu Son Ganin EFCC Ta Binciki Minista

Bello Matawalle: APC Ta Fadi Manufar Masu Son Ganin EFCC Ta Binciki Minista

  • Jam'iyyar APC ta fito ta kare ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle kan zangar-zangar da aka gudanar domin neman EFCC ta bincike shi
  • APC reshen jihar Zamfara ta yi watsi da zanga-zangar wacce ta ce masu shiryata hassada da son rai ne ya yi musu katutu a zukatansu
  • Kakakin jam'iyyar a jihar ya bayyana cewa suna so ne kawai su ɗauke hankalin Matawalle daga sauke nauyin da aka ɗora masa a yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara, ta yi watsi da zanga-zangar nuna adawa da ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle.

Jam'iyyar ta bayyana zanga-zangar a matsayin aikin abokan hamayyar siyasarsa saboda jin zafin tagomashin da yake ƙara samu.

Kara karanta wannan

Binciken Matawalle: An yi sabuwar fallasa kan masu zanga-zanga a EFCC

APC ta caccaki masu son a binciki Matawalle
Jam'iyyar APC ta ce hassada ke damun masu son a binciki Bello Matawalle Hoto: @BelloMatawalle1
Asali: Twitter

Jaridar PM News ta kawo rahoto cewa hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar APC na jihar, Yusuf Idris ya fitar a Abuja ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me APC ta ce kan zanga-zangar?

Kakakin ya bayyana cewa masu kitsa neman ɓata sunan Matawalle, hassada da son rai ne ke damun su, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Yusuf Idris ya bayyana cewa tara wasu ƴan baranda da aka ɗauko haya ba komai zai yi ba face kunyata masu shirya zanga-zangar da ke son ganin hukumar EFCC ta binciki tsohon gwamnan na Zamfara.

Mai magana a madadin APC yake cewa batun da suke magana a kansa surutu ne kawai, domin da akwai gaskiya a ciki da tuni EFCC ta fitar da bayanai a kai.

A cewarsa masu zanga-zangar da waɗanda suka ɗauki nauyinsu sun jahilci dokokin ƙasa, kundin tsarin mulki da yanayin yadda hukumar EFCC ke gudanar da ayyukanta kan waɗanda take zargi.

Kara karanta wannan

Gwamna Dikko Radda ya fadi dalilin gwamnonin Arewa na yin taro a Amurka kan tsaro

Yusuf Idris ya ce manufar masu ɗaukar nauyin zanga-zangar ita ce su ɗauke hankalin Matawalle daga sauke nauyin da aka ɗora masa wajen kawo ci gaba a ƙasar nan.

Batun binciken Matawalle a EFCC

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta bayyana cewa ba ta rufe binciken da take yi kan Bello Matawalle ba.

Kakakin hukumar ya bayyana hakan ne ga masu zanga-zangar neman a sake buɗe binciken da ake yi wa tsohon gwamnan Zamfara, inda ya ce da zarar an fara bincike ba a rufe wa har sai an kawo ƙarshensa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel