Siyasar Najeriya
Yayin da al'ummar jihar Edo ke shirin fita su zabi wanda zai shugabanci su, Legit Hausa ta tattaro maku wasu muhimman abubuwa game da siyasar jihar.
Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya bayyana cewa jam'iyyar PDP za ta amince da sakamakon zaben gwamnan jihar idan an gudanar da shi bisa gaskiya da adalci.
Jam'iyyar PDP ta ce waɗanda suka bar cikinta suka koma APC s jihar Ondo taron ƴan rashin sa'a ne, ta ce ba za su tsinanawa Gwamna Aiyedatiwa da komai ba.
Wasu majiyoyi a fadar shugaban ƙasa sun ce Bola Ahmed Tinubu na iya rusa ma'aikatar jin kai tare da cure wasu hukumomi wuri ɗaya, zai kuma kori ministoci.
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya ce jam'iyyar APC ce ta kitsa rigingimun cikin gida a PDP ta hanyar amfani da tsohon gwamnan Ribas, Wike.
Gwamnan Osun Ademola Adeleke ya ce yana son rawa saboda tana sa shi nishaɗi da farin ciki amma ya fi ƙaunar ya ga yana sauke nauyin da aka ɗora masa.
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya ce shi da sauran gwamnonin PDP sun fara aiki kan yadda za a maido da kujerar shugaban jam'iyya Arewa ta Tsskiya.
Wani rahoto ya nuna cewa wasu gwamnoni 20 na Najeriya sun karbo bashin Naira biliyan 446 domin cike gibin matsalar da suka samu daga kudaden shigarsu.
A kokarin warware rigimar siyasar jihar Ribas, ƴan majalisar amintattu BoT na jam'iyyar PDP sun gana da Nyesom Wike a babban birnin tarayya Abuja ranar Talata.
Siyasar Najeriya
Samu kari