Rikicin PDP
Tsohon gwamnan Delta kuma mataimakin Atiku Abubakar a takarar zaben 2023, Ifeanyi Okowa da wasu jiga-jigan PDP sun koma jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Gwamnatin Akwa Ibom ta musanta rade-radin cewa Gwamna Umo Eno na shirin ficewa daga PDP zuwa APC a kasa bayan takwaransa na Delta, Sheriff Oborevwori ya gudu.
Wani ɗan majalisar wakilan tarayya, Oluwole Oke, ya fice daga jam'iyyar PDP. Sai dai bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba, amma ya nemi mabiyansa da su bar PDP.
Tsohon mataimakin shugaban PDP, Cif Bode George ya nuna takaici kan yunƙurin sauya shekar gwamnoni 4 zuwa APC, ya ce wannan abin kunya ne a siyasa.
Tsohon mataimakin shugaban PDP na ƙasa, Bode George ya nuja damuwa kan yunkurin Atiku Abubakar na sake neman takarar shugaban ƙasa karo na uku a inuwar PDP.
Yayin da ake ta jita-jitar Gwamnan Zamfara zai bar PDP, Dauda Lawal ya fito ya ƙaryata labarin inda ya ce har yanzu shi cikakken dan jam'iyyar ne ba makawa.
Wasu rahotanni sun ce akwai gwamnoni uku ko hudu da ke PDP na shirin sauya sheka zuwa APC, domin marawa shugaba Tinubu baya a yunkurinsa na zarce a 2027.
Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya ce ba zai iya goyon bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ba saboda ba ya mutunta yarjejeniya.
Tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose ya bayyana cewa ba zai goyo bsyan Atiku Abubakar ba a 2027 kamar yadda ya yi a zaɓen 2023, ya ce sai 2031 ɗan Arewa zai karbi mulki.
Rikicin PDP
Samu kari