'Yan Bindiga Sun Bude Wuta kan Magoya bayan Gwamna a Najeriya, An Harbi Mutane 14
- Wasu ‘yan bindiga sun bude wuta kan matasan da ke taron siyasa a Elele, karamar hukumar Ikwerre, inda ake zargin mutum 14 sun jikkata
- Wani ganau ya ce wani jagoran sa-kai ne ya kai harin, kuma har ya yi barazanar kai farmaki kan magoya bayan Gwamna Siminalayi Fubara
- ‘Yan sanda sun cafke mutum daya daga cikin ‘yan bindigar, sun kwace makamin da ya ke hannunsa, suna ci gaba da farautar sauran maharan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ribas - 'Yan bindiga sun farmaki wasu matasa masu taron siyasa a garin Elele, karamar hukumar Ikwerre da ke jihar Ribas, inda suka bude masu wuta.
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba yayin da matasan da ake zargin magoya bayan Gwamna Siminalayi Fubara ne, suka taru don nuna goyon baya ga gwamnan.

Asali: Getty Images
Ribas: 'Yan bindiga sun farmaki masu taron siyasa
Shaidun gani da ido sun ce wani jagoran sa-kai da ake kira ‘Fuccking Naira’ ne ya yi dirar mikiya kan matasan, tare da bude masu wuta, inji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani ganau, mai suna Nwokoro, ya ce wanda ya kai harin jigo ne a wata babbar jam’iyyar siyasa kuma mai goyon bayan wani fitaccen ɗan siyasa.
Yayin da ya yi kira ga hukumomin tsaro su dauki mataki, Nwokoro ya ce 'Fuccking Naira' ya yi barazanar kai wasu hare-hare kan magoya bayan Fubara a nan gaba.
“A kalla mutum 14 ne suka samu raunuka sakamakon harbin bindiga, kuma an garzaya da su asibitin jami'ar Madonna da ke Elele,” inji Nwokoro.
Harin ya zo ne a daidai lokacin da majalisar dokokin Ribas, ƙarƙashin Martin Amaewhule, ta bai wa Fubara wa’adin awanni 48 kan kasafin kuɗi da canja kwamishinonin da ya nada.
'Yan sanda sun yi martani kan farmakin
Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta ce jami’anta sun cafke wani mutum da ake zargi da hannu a harin da aka kaiwa masu taron siyasa a garin Elele.
Punch ta rahoto kakakin rundunar, Grace Iringe-Koko, ta ce mutane hudu ne suka ji raunuka a harin, kuma an garzaya da su asibiti don samun kulawa.
Ta ce sun samu bayanai masu inganci kan taron wasu da ake zargin ‘yan daba ne a wurin, inda jami'ansu suka garzaya wajen don shawo kan lamarin cikin gaggawa.
“A lokacin da ake kokarin saita masu taron, wani mahari da ke ɓuya a yankin ya fito ya fara harbi, wanda ya yi sanadiyyar jikkatar mutane da dama.”
- Grace Iringe-Koko.
Ribas: An cafke daya daga cikin maharan

Asali: Twitter
Ta ce ana ci gaba da bincike, inda har aka samu nasarar kama mutum ɗaya tare da kwace bindiga kirar “single-barrel” daga hannunsa.
Kakakin 'yan sandar ta ce:
"Ya zuwa lokacin fitar da wannan rahoto, mutane hudu ne suka jikkata. 'Yan ta'addar sun watse daga waje, amma an cafke daya daga cikinsu, kuma an kwace bindigar 'single-barrel' daga hannunsa."
‘Yan sanda sun ce za a mika wanda aka kama zuwa sashen binciken manyan laifuka (SCID) yayin da ake ci gaba da farautar sauran ‘yan bindigar.
Kwamishinan ‘yan sanda na Ribas, Olugbenga Adepoju, ya bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu tare da bayar da bayanai masu amfani ga hukumomin tsaro.
'Yan majalisa sun nemi gwamna ya canja kwamishinoni
A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar jihar Ribas ta umarci Gwamna Siminalayi Fubara da ya sake gabatar da sunayen kwamishinoni domin su tantance su.
Majalisar ta rusa dukkanin kwamishinonin da Fubara ya nada a baya, tana mai cewa nade-naden gwamnan na Ribas ya na barazana ga dimokuradiyya ne.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng