Bayan Ƙarewar Wa'adin Sa'o'i 48, Gwamna na Neman Tattago Rigima da Majalisar Dokoki

Bayan Ƙarewar Wa'adin Sa'o'i 48, Gwamna na Neman Tattago Rigima da Majalisar Dokoki

  • Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ba zai mutunta gayyatar da Majalisar Dokoki ta yi masa domin ya sake gabatar da kasafin kuɗin 2025 ba
  • Sakataren gwamnatin jihar, Dr. Tammy Danagogo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ɗauke da kwanan watan 5 ga watan Maris, 2025
  • Ya ce har zuwa jiya Talata, babu wata takarda daga Majalisa a hukumance wanda ke nuna bukatar sake gabatar da kasafin, ya ce a soshiyal midiya suka ji

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers - Gwamnatin jihar Ribas karkashin jagorancin Gwamna Siminalayi Fubara ta ce ba za ta mutunta gayyatar Majalisar dokoki ba.

Gwamnatin ta ce mai girma gwamna ba zai bi umarnin Majalisar Dokokin jihar ba dangane da sake gabatar da kasafin kudin 2025.

Gwamna Fubara.
Gwamnatin Ribas ta yi fatali da gayyatar Majalisar dokoki Hoto: Sir. Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

A rahoton da The Nation ta tattaro, Gwamnatin Ribas ta ɗauki wannan matsaya ne saboda ba ta karɓi wata takarda daga majalisar da ke sanar da bukatar hakan ba.

Kara karanta wannan

Rikici ya ƙara Kamari, jam'iyyar APC ta buƙaci gwamna ya yi murabus cikin sa'o'i 48

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa ta ba gwamna wa'adin sa'o'i 48

Idan ba ku manta ba Majalisar karkashin jagorancin kakakinta, Hon. Martins Amaewhule, ta bai wa Gwamna Siminalayi Fubara wa’adin sa’o’i 48 da ya sake gabatar da kasafin kudin 2025.

Majalisar ta ba gwamnan wannan wa'adi kwanaki ƙalilan bayan kotun kolin Najeriya ta kawo ƙarshen rikicin da ya raba Majalisar dokokin gida biyu.

A hukuncin kotun ƙolin, an tabbatar da Martin Amaewhule da ƴan majalisa da ke tsaginsa a matsayin halastattun mambobin Majalisar dokokin jihar Ribas.

A zaman farko da suka yi bayan hukuncin kotu, ƴan Majalisa sun ba Gwamna Simi Fubara ranakun aiki biyu ya sake gabatar da kasafin kudin 2025.

Gwamnatin Ribas ta maidawa majalisa martani

Sai dai a wata takardar da gwamnatin Ribas ta aike wa Majalisa mai ɗauke da kwanan watan 5 ga watan Maris, ta ce ba za ta mutunta gayyatar da aka yi wa Fubara ba.

Kara karanta wannan

Rabuwar kai a Majalisa, Sanatoci 13 ba su sa hannu a dakatar da Natasha ba

Takardar mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin Ribas, Dr. Tammy Danagogo, ta ce ba ta karɓi wata sanarwa daga majalisar ba, illa dai ta samu labarin hakan ne daga kafafen sada zumunta.

Gwamna Fubara da Amaewhule.
Gwamna Fubara ya sha alwashin bin umarnin doka bayan hukuncin kotun koli Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Martin Amaewhule
Asali: Twitter

A rahoton Leadership, Dr. Danagogo ya ce:

“Har zuwa ƙarshen lokacin aiki a ranar Talata, 4 ga Maris, 2025, ba mu samu takarda a hukumance daga Majalisar Dokoki ba.
"Babu wannan takarda a ofishin gwamna, mataimakin gwamna, ko kuma na Akanta-Janar na jihar."

Gwamna Fubara zai ɗauki matakin da ya dace

Gwamnatin Fubara ta tunatar da majalisar cewa a jawabin da gwamnan ya yi a ranar 2 ga Maris, ya ce, duk da ra’ayinsa kan hukuncin Kotun Koli, zai bi doka kuma zai aiwatar da matakan da suka dace domin moriyar al’umma.

Haka kuma, ta ce lauyoyin gwamnati na jiran takardar hukuncin Kotun Koli, kuma da zarar gwamnan ya samu cikakken bayani, zai aiwatar da matakin da ya dace.

Kara karanta wannan

Majalisar shari'ar Musulunci ta goyi bayan rufe makarantu, ta kirayi jihohi 3 su bi sahu

Rikicin Ribas jarabawa ce daga Allah

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Simi Subara ya ce duk rikicin da ake fama da shi a jihar Ribas ba komai ba ne face jarabawa daga Allah.

Gwamnan ya shaida wa babban limamin coci cewa Allah ya jaraba Ribas da wannan matsala ne domin shi da sauran al'umma su sami cikakken ƴanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng