Gwamna Ya Shiga Matsala, Majalisa Ta ba Shi Awanni 48 Ya Canja Kwamishinoni

Gwamna Ya Shiga Matsala, Majalisa Ta ba Shi Awanni 48 Ya Canja Kwamishinoni

  • Majalisar Ribas ta bai wa Gwamna Siminalayi Fubara wa'adin awanni 48 ya miƙa mata sunayen sababbin kwamishinoni da za a tantance
  • Majalisar ta zargi gwamnan da rantsar da kwamishinoni 19 da wasu jami'ai ba tare da neman amincewarta ba, abin da ta ce ya saɓa wa doka
  • Ta ce nade-naden da Fubara ya yi, suna barazana ga dimokuraɗiyya, tana mai buƙatar a bi tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya da na Ribas
  • Yanzu dai ana jiran martanin Gwamna Fubara kan wannan wa’adin da majalisa ta gindaya masa yayin da rikicin siyasa a jihar ke ƙara kamari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ribas - Majalisar dokokin jihar Ribas ta bai wa Gwamna Siminalayi Fubara wa'adin awanni 48 ya miƙa sabon jerin sunayen kwamishinoni da za a tantance.

A wasikar da ta fitar ranar 5 ga Maris, majalisar karkashin shugaban majalisa, Martin Amaewhule ta zargi Fubara da rantsar da kwamishinoni 19 ba tare da tantancewa ba.

Kara karanta wannan

Mataimakiyar gwamna ta ji wuta, ta yi murabus daga muƙaminta? Bayanai sun fito

Majalisar Ribas ta aika wasika ga Gwamna Fubara kan canja kwamishinoni
Majalisar Ribas ta bukaci gwamnan jihar ya canja kwamishinoni da mukaman da ya raba. Hoto: @SimFubaraKSC, @rvhaofficial
Asali: Twitter

'Yan majalisa sun ki amincewa da nade-naden gwamna

Majalisar ta kuma zargi gwamnan da yin nade-nade a ofisoshin da ke bukatar amincewar majalisar, abin da ta kira saba wa kundin tsarin mulki, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar ta zargi Fubara da naɗawa da kuma rantsar da Dagogo Iboroma a matsayin Antoni-Janar kuma kwamishinan shari’a ba tare da tantancewa ba.

Har ila yau, wasikar ta ce an naɗa Lawrence Oko-Jaja a matsayin shugaban hukumar siyayyar kayayyakin gwamnatin Ribas tare da wasu mutane bakwai ba bisa ka’ida ba.

Majalisar ta ce nade-naden da suka hada da Goodlife Ben a matsayin shugaban hukumar ayyukan kananan hukumomi, tare da wasu mambobi, ba su bi doka ba.

Majalisa ta nemi gwamna ya canza kwamishinoni

Ta ce naɗe-naɗen da gwamnan ya yi, ciki har da waɗanda ba a ambata ba, na barazana ga dimokuraɗiyya, don haka dole ne a canja su cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Neman lalata: Majalisa ta yi watsi da bukatar Natasha kan zargin Akpabio

Majalisar ta bukaci gwamna Fubara ya gaggauta miƙa sunayen sababbin kwamishinoni da sauran mukamai da ke buƙatar tantancewa.

Ta jaddada cewa akwai bukatar gwamnan ya bi tanadin kundin tsarin mulkin 1999 da na dokokin jihar Ribas wajen naɗa jami'an gwamnati.

Ribas: Majalisa ta ba Fubara wa'adin sa'o'i 48

Majalisa ta aikawa Fubara wasikar neman ya canja kwamishsinoni da nade-naden da ya yi
Majalisar Ribas ta fadawa Fubara dokar da zai karya idan bai canja kwamishinoni kamar yadda ta bukata ba. Hoto: @rvhaofficial
Asali: Facebook

Majalisar ta ba Gwamna Fubara wa'adin awanni 48 domin ya gabatar da sababbin sunayen don guje wa ƙara dagula harkokin mulki a jihar.

Wannan rikici na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun rashin jituwa tsakanin majalisar dokokin jihar da gwamnan kan tsarin shugabanci.

A yanzu, ana jiran martanin Fubara kan wannan wa’adin da majalisa ta gindaya masa dangane da nade-naden da ya yi kafin hukuncin kotun koli.

Majalisa ta ba Fubara wa'adi ya bayyana gabanta

A wani labarin, mun ruwaito cewa, majalisar Ribas, ƙarƙashin Martin Amaewhule, ta bai wa Gwamna Siminalayi Fubara wa’adin kwanaki biyu ya sake gabatar da kasafin 2025.

Kara karanta wannan

Yadda Biden da Amurka su ka matsawa Najeriya lamba, aka saki jami'in Binance

Wa’adin ya biyo bayan hukuncin kotun koli da ya tabbatar da tsagin Amaewhule a matsayin halastaccen ɓangaren da ke shugabancin majalisar dokokin jihar Ribas.

A zaman da aka gudanar a Fatakwal, ƴan majalisar sun buƙaci gwamnan ya sake gabatar da kasafin kuɗin domin tantancewa da amincewa da shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng