Jagoran PDP Ya Shiga Fargaba, Ya Hango Yadda Jam'iyyarsa ke Neman Fadawa Hannun APC
- Tsohon sakataren yada labaran PDP, Kola Ologbondiyan, ya bayyana fargabar kan dambarwar shugabanci da ya dabaibaye su
- Ya yi gargaɗin cewa idan Sanata Samuel Anyanwu ya yi nasara a Kotun Koli kan shari’ar sakataren jam'iyya, PDP za ta watse
- Samuel Anyanwu ya na ja da hukuncin kotun da ya tabbatar da Sunday Ude-Okoye a matsayain sakataren PDP na kasa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Tsohon sakataren yada labaran PDP na ƙasa, Kola Ologbondiyan, ya yi gargaɗi cewa idan Samuel Anyanwu ya yi nasara a Kotun Koli kan ƙarar da ya shigar, APC za ta karbe jam'yyarsu.
Ya bayyana haka ne yayin da yake bayani kan takaddamar shugabancin sakataren PDP, yana mai cewa nasarar Anyanwu a Kotun Koli na iya zama abin da zai ƙarfafa ko rusa jam'iyyar.

Asali: Facebook
Ologbondiyan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da Arise News a ranar Talata, tare da gargadin sauran 'yan PDP da su zauna a cikin shirin ko ta kwana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ologbondiyan: "PDP za ta iya samun matsala"
PDP na fama da rikicin cikin gida, wanda har ta kai Samuel Anyanwu ya na ja da Sunday Ude-Okoye a kan kujerar sakataren jam'iyya na kasa.
Da aka tambayi Ologbondinyan abin da zai faru idan Anyanwu ya yi nasara a Kotun Koli, ya ce:
“Ina roƙo da fatan hakan ba zai faru ba, domin zai shafi tushen jam’iyyar PDP. Idan hakan ta faru, tsarin jam’iyyar za ta rushe.”
“Hakan na nufin PDP za ta faɗa hannun APC gaba ɗaya ta hannun Ministan Abuja, Nyesom Wike. Wannan zai zama ƙarshen lamari. Ina baƙin cikin faɗin hakan.”

Asali: Twitter
Ya ƙara da cewa, idan Kotun Koli ta yanke hukunci da ya fifita ɓangaren na jam’iyyar da ba shi da rinjaye a kan mafi yawan membobi, hakan zai haifar da rikici a PDP.
PDP ta zaɓi wanda zai jagoranci jam’iyya
Ologbondiyan ya bayyana cewa kowace jam’iyya ce ke da hurumin zaɓan shugabanninta, kuma PDP ta riga ta tabbatar da wanda zai zama sakatarenta, har an sanar da hukumar INEC.
Ya kara da cewa:
“Jam’iyyar ta riga ta tantance wanda zai zama sakatarenta. Ban san ko kun sani ba, amma PDP ta rubuta wa INEC wasika tana nuna cewa Rt. Hon. S.K Udeh Okoye ne sakatarenta.”
Ya kuma ce babu wata doka da ta dakatar da wannan matsaya, don haka Udeh Okoye ne ya kamata ya ci gaba da gudanar da aiki a matsayin sakataren PDP.
Kotu ta jinkirta yanke hukuncin rikicin PDP
Kotun Koli ta jinkirta yanke hukunci kan ƙarar da Anyanwu ya shigar yana ƙalubalantar cire shi a matsayin sakataren PDP.
Wani kwamitin alkalai biyar, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Uwani Musa Aba-Aji, ne ya ɗauki wannan mataki bayan sauraron hujjoji daga ɓangarorin biyu.

Kara karanta wannan
2027: Yan adawa na shirin firgita Tinubu, ƙusa a PDP ya ce guguwar canji za ta tafi da APC
Kotun daukaka ƙara da ke Enugu ta tabbatar da hukuncin babbar kotu da ta amince da Sunday Udeh-Okoye a matsayin sakataren PDP, inda ta umarce shi da ya karɓi ragamar aiki nan take.
Anyanwu, wanda bai gamsu da hukuncin ba, ya garzaya Kotun Koli a watan Janairu, yana neman a mayar da shi a matsayin sakataren PDP.
2027: Jagoran PDP ya fadi shirin 'yan adawa
A baya, kun ji cewa jagororin jam’iyyun adawa sun fara tattaunawa kan yadda za su kafa haɗin gwiwa domin kalubalantar APC a zaɓen 2027, da manufar tabbatar da ta sha kaye.
Tsohon sakataren yaɗa labaran PDP na ƙasa, Kola Ologbondiyan, ya bayyana cewa wannan shiri ba ƙaramin abu ba ne, tare da bayyana cewa shiryeshirye sun yi nisa a kan kawancen.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng