Gwamna Ya Ƙara Shiga Tsaka Mai Wuya, Majalisar Dokoki Ta Dawo da Shirin Tsige Shi
- Majalisar dokokin jihar Ribas karkashin jagorancin Martin Amaewhule ta sake ɗaukar zafi kan abin da ta kira karya dokokin kundin tsarin mulki
- A wata wasiƙa da suka aike wa Gwamna Fubara ranar Laraba, ƴan Majalisa 27 na tsagin Wike sun yi barazanar hukunta shi kan laifuffukan da ya aikata
- Wannan dai na zuwa ne bayan kotun kolin Najeriya ta tabbatar da ƴan Majalisar a matsayin halastattun mambobin Majalisar Dokokin Ribas
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers - Majalisar dokokin jihar Ribas ta fara yunkurin dawo da shirinta na tsige Gwamna Siminalayi Fubara daga kan kujerarsa.
Hakan dai na zuwa ne bayan rigimar Majalisa da ɓangaren gwamnatin Fubara ta ɗauki sabon salo tun bayan hukuncin kotun ƙolin Najeriya.

Asali: Twitter
Premium Times ta tattaro cewa Majalisar karkashin jagorancin Rt. Hon. Martin Amaewhule ta zargi Gwamna Fubara da karya dokokin kundin tsarin mulkin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan matakin na zuwa ne bayan ‘yan majalisar da ke biyayya ga tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike, sun ba Fubara wa’adin sa’o’i 48 ya sake gabatar da kasafin kudin 2025 a gabansu.
'Yan majalisa na shirin tsige Gwamna Fubara
Zargin karya doka da ake yi wa Gwamna Fubara ya zo ne kwana biyu bayan wa’adin da majalisar ta bayar ya cika ba tare da an sake gabatar da kasafin ba.
Sannan kuma an ji ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa Fubara ya aikata laifukan da za su iya kai shi ga tsige shi daga mukaminsa.
A wata wasika da sakataren gwamnatin Ribas, Tammy Danagogo, ya aika wa majalisar a ranar 5 ga watan Maris, 2025, ce har yanzu gwamnati ba ta karɓi wasikar majalisar ba.
Majalisa ta lissafa laifukan gwamna Fubara
Amma duk da haka, a zaman da suka yi a ranar Laraba, majalisar ta sake aikawa da Fubara wata wasika inda ta lissafa laifukan da ta ce ya aikata na karya doka.
Tun bayan rikicin siyasar da ya barke tsakanin Gwamna Fubara da Wike, majalisar dokokin jihar ta kasu gida biyu, mambobi 27 na goyon bayan Wike, yayin da uku ke bayan Fubara.

Asali: Facebook
Kafin hukuncin da kotu koli ta yanke a ranar Juma’a, Fubara na aika duk wata wasikar gwamnati, ciki har da kudirori da sunayen waɗanda ya naɗa ga tsagin majalisar da ke tare da shi domin tantancewa da amincewa.
Barazanar tsige gwamna ta dawo a Ribas
Wannan ne ya sa ‘yan majalisar da ke goyon bayan Wike suka ce hakan na daga cikin manyan laifukan da gwamnan ya aikata, rahoton Punch.
A wasikar da suka aika wa Fubara, ‘yan majalisar sun ce:
"Muna jaddada maka cewa nada mutane a mukamai ba tare da gabatar da sunayensu don tantancewa da tabbatarwa ba, ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da sauran dokokin kasa."
A ƙarshe, ƴan Majalisar sun yi barazanar ɗaukar matakin da ya dace kan gwamnan bisa karya dokar da ya yi, wanda ka iya jawo tsige shi daga mulki.
Majalisa ta ba Fubara wa'adin awanni 48
A wani labarin, kun ji cewa Majalisar dokokin jihar Ribas ta bai wa Gwamna Simi Fubara wa'adin awanni 48 ya miƙa sunayen waɗanda ya naɗa a matsayin kwamishinoni.
Majalisar ta zargi Fubara da naɗawa da kuma rantsar da mutane da dama a muƙamai daban-daban ba tare da tantancewa ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng