Magana Ta Kare, Kotun Ƙoli Ta Yanke Hukunci kan Ƴan Majalisa 27 da Suka 'Koma' APC

Magana Ta Kare, Kotun Ƙoli Ta Yanke Hukunci kan Ƴan Majalisa 27 da Suka 'Koma' APC

  • Kotun kolin Najeriya ta raba gardama kan taƙaddamar sauya shekar ƴan majalisa 27 na Majalisar dokokin jihar Ribas
  • A shafi na 62 na hukuncin da kotun ta yanke, ta ce babu wata hujja da ke nuna ƴan Majalisar sun fice daga PDP zuwa jam'iyyar APC
  • Kotun ta caccaki Gwamna Siminalayi Fubara bisa tafiyar da harkokin gwamnati ba tare da Majalisa ba, ta ce hakan barazana ce ga demokuraɗiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Kotun Koli ta yanke hukunci cewa babu wata shaidar da ke nuna cewa mambobi 27 na Majalisar Dokokin Jihar Rivers sun fice daga Jam’iyyar PDP zuwa APC.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne saboda Gwamna Siminalayi Fubara, wanda ya yi zargin sauya shekar, daga baya ya janye dukkan takardun da ya shigar a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Kara karanta wannan

2027: Majalisa za ta kafa hukuma domin maye gurbin INEC wajen wasu ayyuka

Martin Amaewhule
Kotu ta ce babu hujjar da ke nuna ƴan Majalisa 27 sun sauya sheka zuwa APC a Ribas Hoto: Martin Amaewhule
Asali: Facebook

Saboda haka, tun da babu wata hujja da ke nuna sun sauya sheka, kotun ta ce a bisa doka, babu wanda ya sauya sheka, kamar yadda The Nation ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan hukunci na nufin cewa har yanzu mambobi 27 na Majalisar Dokokin Jihar Rivers suna kan kujerunsu, kuma dole ne a ci gaba da mutunta matsayinsu.

Kotun Koli ta soki Gwamna Fubara

Kotun Koli ta yi kaca-kaca da Gwamna Fubara, tana mai zarginsa da rushe Majalisar Dokoki ta hanyar rusa gine-ginenta da hana ‘yan majalisa 27 damar gudanar da ayyukansu.

Haka nan kotun ta soki Fubara bisa yunkurin mulki ba tare da majalisa ba, wanda ta kwatanta da mugunta da danniya.

Kotun ta bayyana wadannan ayyuka da cewa saban doka ne kuma barazana ga tsarin dimokuradiyya.

Amaewhule ne kakakin Majalisar Ribas

A cikin hukuncin da Mai Shari’a Emmanuel Agim ya karanta a shafi 62, Kotun Koli ta tabbatar da cewa Martin Amaewhule shi ne halattaccen kakakin Majalisar dokokin jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Natasha ta ja daga, ta nufi kotu kan dakatarwar watanni 6 da majalisa ta yi mata

Kotun ta ce Kundin Tsarin Mulki na 1999 bai amince da ikirarin Gwamna Fubara cewa mutum hudu ne kawai suka rage a matsayin majalisa ba. Kotun ta jaddada cewa:

"Dole ne a samu majalisar da ta cika ka’ida domin gudanar da kowace doka. Zargin sauya sheka da Gwamna Fubara ke yi wani yunkuri ne na hana ‘yan majalisar aiki."
Kotun koli.
Kotun Koli ta tabbatar da Martin Amaewhule a matsayin sahihin kakakin Majalisar dokokin jihar Rivers Hoto: The Supreme Court Of Nigeria
Asali: Facebook

Hukuncin ƙarshe na Kotun Koli

Kotun Koli ta gargadi cewa babu yadda za a yi gwamnati ta yi aiki ba tare da bangarori uku ba — bangaren zartarwa (Gwamna), bangaren majalisa (Majalisar Dokoki), da bangaren shari’a (Kotuna).

Hukuncin ya jaddada rarraba ikon mulki zuwa ɓangarori uku kuma ya hana duk wani yunkuri na mulki na danniya, rahoton Punch.

Bisa wannan hukunci, ƴan Majalisa 27 na tsagin Wike na nan daram a kan kujerunsu, kuma Gwamna Fubara na iya fuskantar karin matsaloli na siyasa da doka a jihar.

Mataimakiyar gwamnan Ribas ta ajiye aiki?

Kara karanta wannan

Majalisar shari'ar Musulunci ta goyi bayan rufe makarantu, ta kirayi jihohi 3 su bi sahu

A baya kun ji cewa mataimakiyar gwamnan jihar Ribas Farfesa Ngozi Odu, ta musanta rahotannin da ke yawo cewa ta yi murabus.

Hakan dai na ƙunshe ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaranta, Owupele Benebo ya fitar da jita-jita ta fara yawo a kafafen sada zumunta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262