Sheikh Aminu Daurawa
Rahotannin da mutane ke yadawa na cewa Malam Aminu Daurawa ya yi murabus daga shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano ba gaskiya ba ne, kamar yadda Legit ta gano.
Gwamnatin Kano ta ce ba za ta tsoma baki a shari'ar da ake yi da shahararriyar 'yar TikTok Murja Kunya ba kamar yadda babu hannunta a sakinta daga gidan yari.
Mansur Ibrahim Sokoto yana ganin babu dalilin gwamnati ta rika fada da ‘yan kasuwan da suka adana kayan abinci a Najeriya ya ce ba su ne su kawo tsadar rayuwa ba.
Malam Ibrahim Khalil ya ce mafi ƙarancin sadaki a yanzu, Naira dubu ashirin, ₦20,000. Sai dai malamin bai kawo hujjojin yadda ya cin ma lissafin ba.
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya shaida cewa an hana su mu’amala da kudinsu da ke banki. Dabarar shi ne za a janye kudi a duk lokacin da suka shigo.
Murja ta fito a sabon bidiyo bayan Hisbah ta ce tana neman waɗansu masu amfani da shafin TikTok bisa laifin furta kalaman batsa cikin wasu bidiyo da suka yi.
Da yake an zartar da hukuncin a ranar Juma’a, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi addu’o’in wajen hudubar sallah a Kano a kan Abba Kabir Yusuf da siyasar Kano.
Wani Malamin addini ya ce zalunci ne a tsige Abba Kabir Yusuf daga mulki duk da yana ganin Abba ya fara mulkinsa da kuskure wajen rushe rushen dukiyar mutane.
Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud ya ce kashe mutane da ake yi a Kaduna ba kuskure ba ne. Shi ma Dr. Sani Umar Rijiyar Lemu ya fitar da jawabi bayan abin da ya faru.
Sheikh Aminu Daurawa
Samu kari