Dalilin da Ya Sa Aka Fitar da Murja Kunya Daga Gidan Gyaran Hali, Gwamnatin Kano Ta Magantu

Dalilin da Ya Sa Aka Fitar da Murja Kunya Daga Gidan Gyaran Hali, Gwamnatin Kano Ta Magantu

  • Gwamnatin Kano ta ce ba za ta tsoma baki a shari'ar da ake yi da shahararriyar 'yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya ba.
  • A cikin wata sanarwa ta hannun kwamishinan watsa labarai na jihar, gwamnantin ta kuma ce ba ta da hannu a sakin Murja daga gidan yari
  • Idan ba a manta ba, an kama Murja tare da kulle ta a gidan gyaran hali biyo bayan tuhumarta da ake yi da laifin yada bidiyon baɗala a TikTok

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta ce ba za ta tsoma baki a shari'ar da ake yi da shahararriyar 'yar TikTok Murja Ibrahim Kunya ba.

Hakazalika, gwamnatin ta ƙaryata jita-jitar da ake yadawa na cewar tana da hannu a cire Murja daga gidan yari a karshen makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Rudani yayin da shahararriyar 'yar Tiktok, Murja Kunya, ta bar gidan yari

Gwamnatin Kano ta magantu kan sakin Murja daga gidan gyaran hali.
Gwamnatin Kano ta magantu kan sakin Murja daga gidan gyaran hali. Hoto: Murja Ibrahim Kunya
Asali: Facebook

Kwamishinan watsa labarai na jihar Kano, Baba Halilu Dantiye ya sanar da hakan a cikin wata sanarwar da ya fita a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ba za ta tsoma baki a shari'ar Murja ba - Dantiye

Baba Dantiye ya ce mutane na yaɗa labaran karya kan cewar gwamnatin Kano ce ta sa aka saki Murja, wacce ake tuhumar ta da laifukan yada bidiyon baɗala da ya sabawa dokar jihar.

Ya yi nuni da cewa an kirkiri wadannan labaran karyar don a bata sunan gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

"Gwamnatin jihar Kano na sane da cewa har yanzu Murja Kunya na gaban kotu kan tuhumar yada bidiyon badala, don haka babu wani dalili da zai saka gwamnatin tsoma baki a ciki.
"Gwamnatin Abba Kabir Yusuf na sane da huruminta da wanda ba nata ba, kuma ba za ta yi katsalandan a shari'ar da ake yi da Murja ba."

Kara karanta wannan

Tinubu ya shiga sabuwar matsala yayin da NLC ta ayyana zanga-zanga na gama gari, an yi karin bayani

A cewar kwamishinan watsa labaran

Dalilin da ya sa aka fitar da Murja daga gidan gyaran hali

Dantiye ya ce gwamnatin jihar ta gano cewa akwai wasu sabbin tuhume-tuhumen da aka shigar akan Murja, wanda ya sa dole aka fitar da ita daga gidan yarin don gudanar da bincike.

Ya ce kotu za ta ci gaba da sauraron shari'ar Murja har zuwa lokacin da za a kai karshen tuhume-tuhumen da ake yi mata.

Da wannan gwamnatin ta yi kira ga jama'a da su kauracewa yaɗa labaran da basu tantance ba musamman wadanda ka iya taba kimar gwamnatin jihar.

Hassan Sani Tukur ya wallafa sanarwar a shafinsa na X.

Me ya sa aka kama Murja Kunya?

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa an gurfanar da Murja Ibrahim Kunya a gaban babbar kotun Shari'a da ke Kwanar Hudu, karamar hukumar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Kotu ta tura mutumin da aka kama da Murja magarkama, zai shafe watanni 6

Ana tuhumar ta ne da laifin yada wani bidiyon tsiraici a shafukanta na sada zumunta wanda ya kai ga kotun ta ba da ajiyarta a gidan gyaran hali.

An dage cigaba da sauraron shari'arta zuwa ranar Talata, 20 ga watan Fabrairu, gabanin kuma aka fitar da ita a karshen makon da ya wuce, wanda ya jawo cece kuce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel