Tsadar Abinci: Shehin Musulunci Ya Soki Tinubu a Kan Rufe Shagunan ‘Yan Kasuwa

Tsadar Abinci: Shehin Musulunci Ya Soki Tinubu a Kan Rufe Shagunan ‘Yan Kasuwa

  • Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto yana ganin babu dalilin da gwamnati za ta rika fada da ‘yan kasuwan da suka adana abinci
  • Farfesan ilmin hadisin ya ce akwai banbamci tsakanin boye abinci da kuma taskance su domin a rika saidawa a kasuwa a hankali
  • Rubutun Mansur Ibrahim Sokoto ya soki yadda Shugaban kasa yake yabo da ba gwamnoni shawawarar koyi da gwamnatin Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Farfesa Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto ya yi tsokaci a game da yadda ake neman magance hauhawar farashin kaya.

Mansur Ibrahim Sokoto ya yi maganganu a shafin Facebook a karshen makon jiya, ya yi tir da matakan da gwamnatoci suka dauka.

Bola Tinubu
Mansur Sokoto ya ci gyaran Bola Tinubu Hoto: Olusegun Dada/Aisar Fagge
Asali: Facebook

Domin ganin an yi maganin yadda ake fama da hauhawar farashin kaya, gwamnatin Bola Tinubu ta fara rufe wasu manyan shaguna.

Kara karanta wannan

Farfesa ya bayyana kuskuren da Tinubu ya fara tafkawa kafin shiga Aso Villa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsarin Shugaba Tinubu da Gwamnan Kano

Baya ga haka, an ji yadda mai girma shugaban kasa Bola Tinubu ya yabi gwamnan jihar Kano, har ya nemi gwamnoni suyi koyi da shi.

Shugaban Najeriyan ya ji dadin yadda ya ga gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta na rufe rumbunan da ake zargin an boye abinci a Kano.

Martanin Mansur Sokoto ga gwamnatin Tinubu

Sheikh Mansur Ibrahim Sokoto yana ganin cewa gwamnatocin nan sun taso manyan ‘yan kasuwa a gaba babu gaira babu dalili kawai.

Fitaccen malamin hadisin ya jefawa gwamnati tambayoyi da ke nuna akwai kuskure a yadda ake neman gyara tattalin arzikin kasar.

Farfesa Mansur Sokoto yana cikin masu ganin ba adana abinci ne ya jawo tashin farashi ba, akwai tasirin tsare-tsaren gwamnati.

Malamin jami’ar ta Usman Danfodio ya tambayi gwamnati ko ba a samun kayan da ake kukan sun yi tsada idan an shiga kasuwanni.

Kara karanta wannan

Gwamna ya kawo shawara 1 rak da ta rage wajen kawo karshen ‘yan bindiga a jihohi

A karshe, shehin malamin ya yi addu’a Allah SWT ya kawo saukin kuncin da aka shiga.

Boye Kayan Abinci ne Yan Kasuwa Suka Yi?

"Na yi mamaki matuka jin cewa, mai girma shugaban kasa ya goyi bayan abin da gwamnatin jihar Kano ta yi na takura ma masu taskace kayayyakin da suke sayarwa na masarufin rayuwa har yana kira ga wasu jihohin su yi koyi da ita."
"Tambayata a nan":
"1. Masu rumbunan abinci su ne suka haifar da yunwa ko tsadar abinci?
2. Idan ba ayi runbun kayan masarufi ba a ina ne za a ajiye kayan da aka sayo daga wasu kasashen kafin a rarraba su a shaguna?
3. Abinci ne kadai ya yi tsada ko har da sauran ababen kamar karfe da katako da zinari da fetur da tufafi dss?
4. Farashin kaya ne ya tashi ko darajar Naira ce ta sauka? Idan Naira ce ta lalace wa ya lalatar da ita?

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya ki karbar shawarar bude iyakoki da kayyade farashin abinci

5. Kayan da ke a Store an neme su a kasuwa ne aka rasa bale ace boyewa su aka yi?"
"Ina gudun a bar dukan "Sa" a dawo bugun taiki. Masu mulki sun san in da matsalar tsadar rayuwa take; su daina yin zaluncin da zai kara shigar da mu wata sabuwar damuwa.
Ya Allah!"
"Muna tawassuli da addu'oin bayinka duk da suke cikin matsatsi a Najeriya da sauran kasashe ka yaye mana wannan musiba ta hanyar da ka fi amincewa da ita."

- Sheikh Mansur Ibrahim Sokoto

Farfesa ya ce Tinubu ya yi kuskure

Ana da labari Farfesa Kabiru Isa Dandado ya ce ‘yan Najeriya ba za su iya jure wannan hauhawar farashin kaya da ake fuskanta a yau.

Masanin tattalin arziki ya ce Bola Tinubu ya yi kuskuren yi maganar cire tallafin fetur da kuma yanzu da aka kawo zancen rufe shaguna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel