Addu’o’i 4 da Sheikh Daurawa Ya yi wa Abba Gida Gida da Kotu Ta Tabbatar da Kujerarsa

Addu’o’i 4 da Sheikh Daurawa Ya yi wa Abba Gida Gida da Kotu Ta Tabbatar da Kujerarsa

  • Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya taya Abba Kabir Yusuf murnar nasarar da ya yi a shari’ar Kano
  • Kotun koli ta tabbatar da gwamna Abba ne halataccen gwamna, aka soke gaskiyar da aka ba APC
  • Aminu Ibrahim Daurawa ya rokawa Abba Kabir Yusuf sa’a, kuma ya yi kira ga Nasiru Yusuf Gawuna

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi wa Abba Kabir Yusuf addu’a bayan nasarar da shi da NNPP suka samu a kotun koli.

Shugaban hukumar ta Hisbah ya yi addu’o’in ne tun a makon da ya gabata, jim kadan bayan hukuncin da alkalai suka yi a birnin Abuja.

Abba - Daurawa
Gwaman Kano da Aminu Daurawa Hoto: Abba Kabir Yusuf/Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Asali: Facebook

Abba ya yi nasara ranar Juma'a

Da yake an zartar da hukuncin ne a ranar Juma’a, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi addu’o’in a babban masallacin jami’ar Skyline.

Kara karanta wannan

Yadda muka taimaki APC aka haifar da Gwamnatin Buhari a 2015 - Tsohon Gwamnan PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shehin ya fara ne da yi wa gwamnan jihar Kano addu’ar Ubangiji Madaukakin Sarki SWT ya hada shi mashawarta nagari a gwamnati.

Aminu Ibrahim Daurawa ya kuma roki Allah SWT ya taimakawa mai girma Abba Kabir Yusuf wajen cigaba da ayyuka na alheri.

Har ila yau, babban malamin musuluncin ya roki Ubangiji SWT ya sa gwamnan ya yafewa kowa, ya guji daukar fansa a kan makiyansa.

Malamin ya tunawa Abba Gida Gida shi gwamnan kowa ne ba tare da la’akari da wadanda suka mara masa baya ko akasin haka ba.

“Idan Allah ya ba ka nasara, ba ka da abokin fada kuma."

- Aminu Ibrahim Daurawa

Sannan Aminu Daurawa ya kawo maganar maida hankali wajen cigaban Kano da al’ummarta da duk abin da zai zama alheri.

Hudubar Sheikh Daurawa ta kunshi addu’ar nasara a mulki, ya nemi Allah SWT Ya taimaki gwamnatin NNPP da ta lashe zaben 2023.

Kara karanta wannan

Kwanaki 5 da hukuncin Kotun Koli, Sarakuna 4 sun ki taya Abba murnar galaba kan APC

Kamar yadda bidiyon hudubar da aka wallafa a Facebook ta nuna, Daurawa ya nemi ka da Allah SWT ya bar Abba da dabarunsa.

Da yake addu’ar a makon da ya gabata, Daurawa ya kuma roki Allah SWT ya hana gwamna yin duk abin da zai iya zama sharri.

Kira ga masoya da 'yan adawa a Kano

A karshe ya nemi wadanda ba suyi nasara ba su hada-kai domin a kawowa Kanawa alheri, ya ce addini da jihar Kano ce a gaba da komai.

Sheikh Daurawa ya ce siyasa ta zo karshe sai nan gaba, ya bukaci magoya baya su guji yin izgili saboda wani bangare bai samu gala ba.

Abba zai kori Sarakunan Kano?

Ana da labari jagora a NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya tabo batun Sarakunan da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta kirkiro.

A shekarar 2019 aka kawo karin sarakuna a Bichi, Gaya, Karaye da Rano a mulkin APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel