Ba Za Mu Yarda Ba: Rayuwar Murja Kunya Tana Fuskantar Barazana Inji Lauyoyi

Ba Za Mu Yarda Ba: Rayuwar Murja Kunya Tana Fuskantar Barazana Inji Lauyoyi

  • Barista A. U. Haji ya soki yadda ake bi wajen warware shari’ar Murja Ibrahim Kunya da hukumar Hisbah a kotun musulunci
  • Jagoran lauyoyin da ke kare wannan ‘yar tik tok ya ce kawunta ya sanar da su cewa an nemi yi mata allura da karfin da yaji
  • Lauyan ya ce kotu ba ta bada umarni yi wa Murja Kunya magani ba, hurumin likitoci shi ne su yi mata gwajin lafiya kurum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Barista A. U. Haji wanda ya tsayawa Murja Ibrahim Kunya a kotu, ya kawo kukan cewa suna fuskantar babbar barazana.

Gidan rediyon Freedom da ke garin Kano ya rahoto A. U. Haji yana bada labarin abin da ya faru da Murja Ibrahim Kunya a asibiti.

Kara karanta wannan

Oronsaye: Wasu ma’aikatu da hukumomi 45 da Gwamnatin tarayya za ta iya rusawa

Murja
Hisbah tana shari'a da Murja Kunya a kotun musulunci a Kano Hoto: Murja Ibrahim Kunya
Asali: Facebook

Shugaban lauyoyin Murja Kunya

Jagoran lauyoyin wannan baiwar Allah a karar da ake yi a kotun shari’a ta kwana hudu PRP ya ce an hana su ganin Murja Kunya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkali ya bukaci a kai wannan ‘yar tik tok asibiti domin a duba lafiyar kan ta, amma da aka je asibitin, sai ta ki bari ayi mata allura.

Kamar yadda Barista A. U. Haji ya shaida, Murja Kunya ta damko masoyinta da ake neman yi mata allura, tace sai dai a yi masu tare.

Murja Kunya: Lauyoyi sun fara koke-koke

“Muna ganin cewa matakin da ita hukuma ko hukumar kula da asibitoci na jihar Kano ta dauka a halin yanzu kuskure ne.”
“Rayuwar wanda muke ba kariya tana cikin hadari, tana cikin hadari sosai.”
“Kowace irin tuhuma ake yi mata, abin da kotu ta ce shi ne a je a duba lafiyarta. Duba ta za a yi ba magani za a yi mata ba.”

Kara karanta wannan

Sabuwar dokar CBN ta jawo surutu a yunkurin maido darajar Naira a kan Dala

- A. U Haji

Lauyoyi Murja ba za su zura ido ba

Aminiya ta rahoto Haji yana sukar matakin da alkalin kotu ya dauka, ya kuma ce ba za su bari mummunan abu ya faru ba.

A cewarsa an kai Murja asibiti Dawanau, daga bisani aka kawo ta asibiti a Nasarawa, kuma ya kamata a samu rahoton gwajin.

Haji ya ce dokoki sun ba wanda Hisbah ta ke tuhuma damar sanin larurarta, a ra’ayin tun farko babu dalilin cewa a tafi asibiti.

Lauyoyin Murja za su kai gwamnati kotu?

Lauyoyin da ke kare Murja Kunya sun yi barazanar maka gwamnatin Kano a gaban alkali a rahoton da muka samu a baya.

A cewar lauyoyin, sun ba gwamnatin wa’adin awanni 24, sun ce duk mutumin da ake tuhuma yana da ‘yancin ganin lauya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel