Murja Kunya Ta Aikawa Hisbah Sako Yayin da Aka Bada Cigiyar Nemansu a Kano

Murja Kunya Ta Aikawa Hisbah Sako Yayin da Aka Bada Cigiyar Nemansu a Kano

  • Murjanatu Kunya tayi fice a dandalin Tik Tok, wanda hakan ya sa hukumar Hisbah ta zauna da ita
  • Yanzu hukuma tana neman ‘yar Tik Tok din da wasu mutane saboda zargin yin kalaman batsa a bidiyo
  • Kwatsam sai aka ga wani bidiyon Murja yana yawo inda ake tunanin ta maidawa Hisbah martani ne

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Murjanatu Ibrahim Kunya wanda ta fi shahara da Murja Kunya ta maida martani yayin da aka ji ana nemanta.

Murja Kunya a wani bidiyo da aka wallafa a shafin Facebook tayi wa hukumar Hisbah raddi da cewa sun san inda ta ke.

Murja Kunya
'Yar Tik Tok, Murja Kunya Hoto: Murjanatu Ibrahim Kunya
Asali: Facebook

An san inda Murja Kunya ta ke?

Kara karanta wannan

"Baturiya na ke son Allah ya hallito ni idan zan sake zuwa duniya", In Ji Jarumar Fim Na Najeriya

Shahararriyar ‘yar Tik Tok din ta fito baro-baro a bidiyo tana mai cewa makwancinta ba wani boyayya ba ne ga hukuma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Murja ta nuna babu abin da ya dame ta domin daga kalamanta za a ji tana bayanin za ta koma gado ne ta cigaba da barci.

Wannan mata tace babu abin da zai sa ta saba alkawari, ta kuma yi ga barazana ga mai karya alkawarin da ya dauka da ita.

Jawabin Murja Kunya a Tik Tok

"Duk wanda yace ana neman Murja karya yake yi domin an san inda nake, an san inda Murja take.
"An san makwancinta (Murja) kuma kowa ya san inda Murja take, saboda haka wannan maganar karya kuke.
"Idan kuwa haka ne an san inda nake a zaune, an san inda nake barci, yanzu haka ma barci zan komawa"

- Murjanatu Ibrahim Kunya

Kara karanta wannan

"A nemo mun ita: Bidiyon wata yar makaranta tana Sallah a kan hanya ya dauka hankalin jama'a

An samu wannan bidiyo ne daga shafin @Yagame1 a shafinna Tik Tok sai Abba Gwale ya daura fai-fen kan Facebook.

Daurawa da Hisbah za su canza salo?

Tun da sanarwar ta fito wasu suka rika nuna babu dalilin Hisbah ta bada cigiya alhali an san inda za a iya cafko mutanen nan.

Wasu mutanen Kano sun nuna matakin ruwan sanyin da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya dauka bai magance matsalar ba.

Bayan nada shi shugaban Hisbah, Sheikh Aminu Daurawa yayi zama da ‘yan tik tok, ya ja hankalinsu game da abin da suke yi.

Murja Kunya ta gagara ne?

Kwanaki aka ji Murja Ibrahim Kunya ta nemi a daina yi mata zancen aure, hakan ya biyo bayan auren da gwamnati ta shirya a Kano.

Duk wanda ya tunkari wannan mata da zancen aure, tace sai dai ya ji kutufo saboda ta na da bakaken aljanu da ke da wahalar sha'ani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel