Kano: Kwankwaso Ya Yi Martani Kan Murabus Din Daurawa Daga Shugabancin Hisbah, Ya Yi Gargadi

Kano: Kwankwaso Ya Yi Martani Kan Murabus Din Daurawa Daga Shugabancin Hisbah, Ya Yi Gargadi

  • Yayin da Malam Aminu Daurawa ya yi murabus daga kujerarsa, jigon APC, Musa Ilyasu Kwankwaso ya yi martani
  • Kwankwaso ya ce wannan addini aka taba tun da malami ne mai wa’azi tun da har fatan alkairi ya yi wa Gwamna Abba
  • Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir ya kushe tsarin da hukumar ke bi yayin ayyukanta inda ya ce bai dace ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Jigon jam’iyyar APC, Musa Ilyasu Kwankwaso ya yi magana kan murabus din Malam Aminu Dauraa da ya yi.

Musa Kwankwaso ya ce ba za a taba bari Daurawa ya yi gyara ba sai dai ya sauka idan dai a kan su Murja ne ko Kannywood.

Kara karanta wannan

Hisbah Kano: Tsohon hadimin Buhari ya magantu kan murabus ɗin Sheikh Daurawa

Kwankwaso ya yi magana kan murabus din Daurawa a shugabancin Hisbah
Kwankwaso ya ce daman ya fada a baya ba za su bar Daurawa ya yi aiki ba. Hoto: Ilyasu Kwankwaso. Abba Kabir, Aminu Daurawa.
Asali: Facebook

Menene Kwankwaso ke cewa kan Daurawa?

Ya ce daman a baya ya fada cewa kyan Daurawa ya sauka kuma yanzu ta tabbata inda ya ce ba adawa ya ke yi ba halinsu ya sani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa burin ‘yan Kwankwasiyya shi ne azabtar da mutane a ci mutuncin mutane da keta addini da kuma sharholiya.

Jigon APC ya bayyana haka ne yayin hira da DCL Hausa da safiyar yau Juma’a 1 ga watan Maris inda ya ce Daurawa ya yi abin kirki.

“Malam Daurawa ya yi abinsa tsakani da Allah, na sha fada a baya Malam Daurawa mutumin kirki ne, ba na Kwankwasiyya amma ina yabonsa.
“Abin da muke fada komai ka yi don Allah idan ba za kayi ba, to kayi shiru da bakinka, su ba dan Allah suke yi ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano ya karya gwiwar Sheikh Daurawa, ya yi murabus daga shugabancin Hisbah

“Mutane su bar bata lokaci da cece-kuce a kan wannar magana za a ga abin da ya fi wannan lalacewa idan ba a gyara ba.”

- Ilyasu Kwankwaso

“Indai a kan Murja ne da ‘yan Kannywood sai dai Daurawa ya sauka ba za a bari ya yi gyara ba, na fada kuma ta tabbata.”

- Ilyasu Kwankwaso

Daurawa ya yi murabus

Kun ji cewa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi murabus daga kujerar shugabancin Hukumar Hisbah.

Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir ya kushe tsarin da hukumar ke bi yayin ayyukanta inda ya ce bai dace ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel