Shugaban Malamai Ya Yi Fatawar Da Ta Karya Sadakin Aure Daga N100,000 Zuwa N20,000

Shugaban Malamai Ya Yi Fatawar Da Ta Karya Sadakin Aure Daga N100,000 Zuwa N20,000

  • Malam Ibrahim Khalil ya soki masu biyewa lissafin kalanda, ana harba sadakin aure zuwa kusan N100, 000
  • Shehin ya yanke mafi karancin sadaki a kan N20, 000, sai dai bai kawo hujjojin yadda ya cin ma lissafin ba
  • Ganin rayuwa tayi wahala, Sheikh Ibrahim Khalil yana ganin akwai kuntatawa idan aure ya yi tsada sosai

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Ibrahim Khalil wanda babban malamin addinin musulunci ne ya shiga labarai sabod wata fatawa da ya bada.

An yi wa Sheikh Ibrahim Khalil tambaya a game da mafi karancin sadaki, abin mamaki sai ya bada amsa da N20, 000.

Malam Ibrahim Khalil
Malamin addini ya karya sadaki Hoto: Malam Ibrahim Khalil, Getty
Asali: Facebook

Kamar yadda bayanin yake a shafin Khalil Network na Facebook, malamin ya bayyana hikimar rage kudin auren.

Kara karanta wannan

Sanata ya fadakar da mutane a kan hanyoyi 3 da za a bi domin karya Dalar Amurka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fatawar shugaban majalisar malaman ta sabawa lissafin kwamitin ganin wata da ya yanke sadaki yanzu a kan N99, 241.

Malamin ya ce masu amfani da N99, 000 ko N100, 000 a matsayin karancin sadaki ba su da fahimtar addinin musulunci.

Ibrahim Khalil bai yarda da farashin Dala ba

Ibrahim Khalil ya kafa hujjar addini ya nemi a saukakawa al’umma idan an shiga matsi kuma ya soki tashin dala a yau.

Malamin yana ganin IMF da manyan duniya suka tilasta aka saki Dala a kasuwa, saboda haka dole kimar Naira ta karye.

"Kuma abin da za ka gane, canjin dala na yanzu ba na hakika ba ne, canjin dala ne na larura da masifa ta shigo da shi, ba za ayi aiki da su ba."

- Sheikh Ibrahim Khalil

Mecece hujjar Ibrahim Khalil a kan sadaki

Kara karanta wannan

Zanga-zanga sun tada hankalin Gwamnati, Shugaban kasa ya dauki mataki a guje

"Na farko ka’ida ta ce idan abubuwa sun yi kunci, a saukaka shi. Yanzu idan ka ce a biya N90, 000, mutum nawa zai biya N90, 000."
"Ina ga ka tafi kauye (wa zai iya biyan N100, 000)."
"Idan kayi maganar kayan lefe, a rana daya ake yin kayan lefe?

- Sheikh Ibrahim Khalil

Za a iya biyan fiye da N20, 000 a sadaki?

A bidiyon, malamin ya ce mai hali zai iya bada abin da ya zarce N20, 000 wajen aure bayan wani ce-ce-ku-ce da aka yi.

Tsohon ‘dan takaran gwamnan yake cewa a sahaban Annabi SAW akwai wadanda suka biya sadaki na fiye da N10m.

Tarar N20 ko zaman gidan yari

Rahotanni sun ce Alkali Abdul Hamid ya yanke hukuncin biyan tarar N20 ko daurin shekaru uku a babban kotun jihar Gombe.

Mai shari’a ya samu Rose Dogara Silas Gyar da laifin karbar N3m a hannu wani domin nemo masa bashin kaya daga CBN.

Asali: Legit.ng

Online view pixel