Hisbah Kano: Tsohon Hadimin Buhari Ya Magantu Kan Murabus Ɗin Sheikh Daurawa

Hisbah Kano: Tsohon Hadimin Buhari Ya Magantu Kan Murabus Ɗin Sheikh Daurawa

  • Bashir Ahmad, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Buhari, ya ce bai kamata Gwamna Abba ya fadi laifin Hisbah a bainar jama'a ba
  • A cewar Bashir Ahmad, kalaman gwamnan akan ayyukan hukumar Hisbah ya yi dai dai da abin da Hausawa ke cewa 'kwance zani kasuwa'
  • Legit Hausa ta tattaro ra'ayoyin jama'a kan murabus din Sheikh Aminu Daurawa daga shugaban hukumar Hisbah ta Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano - Tsohon hadimin Buhari ta fuskar kafofin sada zumunta, Bashir Ahmad, ya yi tsokaci kan murabus din Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa daga shugaban hukumar Hisbah Kano.

Bashir Ahmad ya ce "Abba ya kwancewa Hisbah zani a kasuwa" shi ya sa Sheikh Daurawa ya hakura ya ajiye aikin na sa.

Kara karanta wannan

Kano: Kwankwaso ya yi martani kan murabus din Daurawa daga shugabancin Hisbah, ya yi gargadi

Bashir Ahmad ya magantu kan ajiye aikin Daurawa
Bashir Ahmad ya ce bai kamata Gwamnan Kano ya fadi laifin Hisbah ba. Hoto: @BashirAhmaad, @ibrahim_daurawa
Asali: Twitter

Daurawa ya yi murabus daga shugaban hukumar Hisbah

Legit Hausa ta ruwaito cewa kwamandan hukumar Hisbah na jihar Kano, Sheikh Aminu Daurawa ya yi murabus a ranar Juma'a, 1 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daurawa ya wallafa sanarwar murabus dinsa a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta a safiyar Juma'a.

Murabus din Daurawa na zuwa ƙasa da awanni 24 bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya zargi hukumar da cin zarafin mutane da sunan yaƙi da baɗala.

Sheikh Daurawa ya yi wa Gwamna Yusuf martani

Gwamna Yusuf ya ce matakan da Hisbah ke dauka na cafke masu laifi, lalata kayayyaki ya saba wa ƙa'ida yana mai jaddada bukatar hukumar ta sake fasalin ayyukanta.

Sai dai da ya ke martani kan zargin gwamnan, Daurawa ya bayyana cewa hukumar Hisbah a karkashin jagorancinsa ta yi aiki tuƙuru don gyara tarbiyar ɓata gari a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano ya karya gwiwar Sheikh Daurawa, ya yi murabus daga shugabancin Hisbah

A cewar Sheikh Daurawa, babu wani mataki da Hisbah ta dauka wanda ya saɓa da dokar addinin Musulunci, yana mai sanar da murabus dinsa daga shugaban hukumar.

Bashir Ahmad ya yi martani kan murabus ɗin Daurawa

Da ya ke martani kan abubuwan da ke faruwa a Kano, Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na X cewa:

"Al'umma ba za su taɓa mutunta shugaban da zai fito fili yana faɗin aibun ma'aikatansa ba, sanin kowa ne Hisbah da kwamandanta na aiki karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ne.

A wata wallafar kuma, Ahmad ya ce:

"Maimakon ya fito fili ya ƙasƙantar da ikon hukumar Hisbah, kamata ya yi Gwamna Abba ya kira Daurawa su yi magana kai tsaye, hakan ne kawai zai kare martabar kowa."

Abin da mutane ke cewa:

Nuhu Adc ya ce:

Abu baiyi dadi ba, Amma mutumci shine gaba.
Allah ya kara ma Malam lafiya

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Buhari ya nemi Gwamnatin Abba tayi koyi da Gwamnonin jihar Legas

کبير إبراهیم حسین ya ce:

Wallahi wannan ba karamar musiba ba ce ga duk mai hankali.
Kamawa ko cakumar masu badala duk acikin gyara ne
“Duk wanda ya keta alfarmar Allah bashi da wata sauran alfarma”

Alhassan Bin Sulaiman ya ce:

Alhamdulillah allah ya kara wa malam Aminu Daurawa lafiya da nisan kwana masu albarka, gara da ya ajiye musu kayansu tunda ba gyaran al'umma bane agabansu bah.

Abdul Maude ya ce:

Malam abinda kayi shine dai dai. Da ka bari a sabawa dokar Allah da keta ka'dar alkawarin aiki don son duniya gwara ka bar musu.

Lawan Abdullahi Yahaya ya ce:

Malam aminu munshaida cewar addini kayiwa aiki a gwamnatin Abba kabir yusif Dan muna da kyakykyawan zato akan bazaka wulakanraba ko awajen ubangiji Allah subahanahu wataala

Abin da Gwamna Abba ya fadawa malaman Kano

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya gana da malaman addinin Musulunci na jihar Kano yayin da ake shirin shiga watan Ramadan.

Yayin da gwamnan ya nuna rashin jin dadin yadda ake yi wa malamai rikon sakainar kashi, ya kuma roke su da su rinƙa ankarar da shi idan ya yi kuskure a mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel