Daurawa Ya Yi Murabus Daga Shugabancin Hisbah? An Samu Karin Bayani

Daurawa Ya Yi Murabus Daga Shugabancin Hisbah? An Samu Karin Bayani

  • Shafukan sada zumunta sun cika da labarai na fargabar Mallam Aminu Daurawa ya yi murabus daga shugaban Hisbah, Kano
  • Wannan murabus din da ake zargin Daurawa ya yi, ba zai rasa nasaba da rahotannin cewa an fitar da Murja Kunya daga gidan yari ba
  • Sai dai Legit Hausa ta tuntubi hukumar Hisbah kan lamarin, wadda ta tabbatar da cewa, Daurawa bai yi murabus ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Tun bayan da aka gano cewa fitacciyar 'yar TikTok, Murja Kunya ta shaƙi iskar 'yanci daga gidan gyaran hali kafofin sada zumunta suka ɗauki zafi kan maganar.

A safiyar yau kuma aka tashi da fargabar Malam Aminu Daurawa, ya yi murabus daga shugaban hukumar Hisbah ta Kano, saboda an saki Murja.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa aka fitar da Murja Kunya daga gidan gyaran hali, gwamnatin Kano ta magantu

Karin haske kan rade-radin Mallam Daurawa ya yi murabus daga shugaban hukumar Hisbah.
Karin haske kan rade-radin Mallam Daurawa ya yi murabus daga shugaban hukumar Hisbah. Hoto: Murja Ibrahim Kunya, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Asali: Facebook

A yayin da batun sakin Murja daga gidan gyaran hali ka iya zama gaskiya, sai dai, akwai rudani a rahoton cewa Daurawa ya yi murabus daga shugaban Hisbah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daurawa bai yi murabus ba, in ji hukumar Hisbah

Wata majiya daga hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta shaidawa Legit Hausa ta wayar tarho cewa Mallam Aminu Daurawa bai yi murabus daga shugaban hukumar ba.

Majiyar ta tabbatar da cewa ko yau Litinin, Daurawa ya yi aiki a ofishinsa da ke a hukumar, wanda ya nuna cewa jita-jita kawai mutane ke yadawa.

A cewar majiyar:

"Ko yanzu da nake maka magana Mallam Daurawa na cikin ofishinsa yana aiki. Ka san kuwa duk wanda ya yi murabus ba zai je wajen aiki ba.
"Magana kan an saki Murja Ibrahim Kunya daga gidan gyara hali ba hurumin Hisbah ba ne ta yi magana akai, wani al'amari ne da ya shafi kotu da masu gabatar da kara."

Kara karanta wannan

Aiki na shine na biyu mafi wahala a duniya, Gwamnan CBN Cardoso

Mutane sun roki Daurawa ya yi murabus

Abbas Ibrahim Dalibi, ya ce bai kamata Daurawa ya ci gaba da shugabantar Hisbah ba ma damar ta tabbata Murja Kunya ta fita daga magarkama.

"Mallam ya sauke nauyin da Allah ya daura masa, amma ba za a kyale shi ya yi aiki yadda ya kamata ba, don haka ya yi murabus ya koma ya cigaba da yin wa'azi matsayinsa na malami."

Bin Yakub ya ce akwai bukatar gwamnatin Kano ta sani cewa Malam Aminu Daurawa ya fi daraja a wajen al'umma fiye da gwamnati balle Murja.

"Duk wani mutum mai mutunci ba zai kalli Murja da mutunci ba, kuma matakin da gwamnati ta dauka ba tirbar addini ba ce."

Shi kuwa Muhammad B Lawal ya ce:

"Ina goyon bayan Daurawa ya yi murabus daga matsayinsa na shugaban Hisbah tun da dai gwamnatin Kano ta saki Murja Ibrahim Kunya."

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya magantu yayin da wasu mata suka yi zanga-zanga zigidir saboda tsadar rayuwa

Bidiyon wa'azin Daurawa ya jawo magana

Tun da fari, Malam Aminu Daurawa ya yi wani wa'azi, wanda ya ke nuna cewa duk wanda ya fi karfin hukuma to bai fi karfin Allah ba, wanda wasu ke ganin cewa da Murja Kunya ya ke.

Bidiyon wa'azin malamin ya yadu ne bayan da labarin sakin Murja daga kurkuru ya bazu a gari, inda aka ji malamin na cewa ko a zamanin Banu Isra'ila, an samu irin wannan matsalar.

Kalli bidiyon a kasa:

Kasuwar Shehu Ng ya yi martani kan wannan bidiyon, inda ya ce duk wanda bai ji dadin kalaman Daurawa ba to "munafiki ne ko kuma ya jahilci addini."

Aliyu U. Tilde ya rubuta cewa:

"Ka ci gaba da aikin alkairi Mallam. Ka yi abin da za ka iya, su ma su yi abin da za su iya, ba wai akan 'yan TikTok ba, duk aikin ka a Hisbah wani aikin lada ne da Allah kadai zai biya ka."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 9, sun sace tsohon daraktan CBN da wasu 34 a jihar Arewa

Kotun Musulunci ta garkame Murja a gidan gyaran hali

A makon da a gabata ne Legit Hausa ta ruwaito cewa wata kotun Musulunci ta ba da umurnin tsare Murja Kunya a gidan gyaran hali.

Wannan hukunci ya biyo bayan shigar da ita kara da aka yi akan tuhumar yada badala da ayyukan karuwanci.

Kuma kotun ta yanke hukuncin wata shida a gidan gyaran hali ga mutumin da aka kama shi yana lalata da Murja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel