Matasan Najeriya
A makon nan ne kwatsam aka ji yadda Rarara ya saki sabuwar da ke yabawa gwamnatin Bola Ahmad Tinubu duk da halin da ake ciki na yunwa da fatara a Arewa.
Fitaccen malamin addinin Musulunci ɗan asalin ƙasar Sudan ya ja kunnen matasan Najeriya da kar su yi kuskuren ba maƙiya dama su shigo su ruguza ƙasar su.
Fitaccen mawaki Habeeb Okikiola da aka fi sani da Portable ya dira kan masu zanga-zanga inda ya ce talauci da rashin aiki ne yake saka matasan ke son fita.
Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya kira wata ganawa da shugabannin APC a jihohi 36 a kasar yayin da ake shirin shiga zanga-zanga na halin kunci.
Kungiyar kwadago TUC ta bayyana cewa ba ta da shirin shiga zanga zangar tsadar rayuwa da ake shirin yi a faɗin Najeriya saboda babu wanda ya sanar da ita.
Tsohon daraktan hukumar DSS, Mike Ejiofor ya yi martani kan zanga-zanga a lokacin mulkin Goodluck Jonathan da kuma wanda za a yi yanzu kan halin kunci.
Jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya gargadi masu shirin yin zanga zanga su sake tunani domin gujewa illar da hakan zai haifar kamar asarar rayuka.
Gwamnan Kaduna Malam Uba Sani ya shawarci sarakuna watau shugabannin al'umma su wayar da kan mutane kan illar zanga-zangar da ake shirin yi a watan Agusta.
Babban Sifetan 'yan sanda a Najeriya, Kayode Egbetokun ya ba matasa masu shirin zanga-zanga damar gudanar da ita cikin lumana amma tare da gindaya wasu sharuɗa.
Matasan Najeriya
Samu kari