Minista Ya Fadi Abin da Tinubu Ke Bukata Kaɗai Daga 'Yan Najeriya Domin Inganta Kasar

Minista Ya Fadi Abin da Tinubu Ke Bukata Kaɗai Daga 'Yan Najeriya Domin Inganta Kasar

  • Mohammed Idris, Ministan yada labarai a Najeriya ya ce Shugaba Tinubu na buƙatar hadin kai daga 'yan kasar
  • Idris ya ce Tinubu ya kawo tsare-tsare domin inganta rayuwar al'ummar kasar wanda ya ke bukatar goyon bayansu
  • Minista Idris ya bayyana haka ne a jiya Asabar 13 ga watan Afrilu inda ya ce komai zai daidaita a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya fadi babban abin da Shugaba Bola Tinubu ke buƙata daga 'yan Najeriya.

Ministan ya ce Tinubu na buƙatar haɗin kan 'yan kasar domin inganta rayuwarsu da sauya fasalin kasar gaba daya.

Ministan Tinubu ya bayyana abin da shugaban ke bukata daga 'yan Najeriya
Minista Idris ya ce Shugaba Tinubu na buƙatar hadin kan 'yan Najeriya domin inganta rayuwarsu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Wasu tsarte-tsare Tinubu ya kawo Najeriya?

Kara karanta wannan

Kano: Abba Kabir ya dauki zafi bayan sakin 'yan daba daga kulle, ya sha alwashi kan lamarin

Idris ya bayyana haka ne a jiya Asabar 13 ga watan Afrilu a Kaduna yayin wani babban taro, cewar rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce gwamnatin ta kawo tsare-tsare da za su inganta al'umma inda ya ce kawai hadin kai suke bukata daga 'yan kasar.

Ya kara da cewa rarar kudi da aka samu bayan cire tallafin man fetur sun kara inganta bangaren noma, kamar yadda NAN ta tattaro.

Ministan ya yabawa Tinubu bangaren tsaro

A bangaren tsaro, ministan ya ce Shugaba Tinubu ya yi namijin kokari wurin dakile matsaloli da dama inda ya yabawa jami'an tsaro kan gudunmawa da suke bayarwa.

Ya kuma godewa shugaban kan irin goyon bayan da ya ke ba ma'aikatarsa inda ya ce hakan ya taimaka wurin samun ci gaba a bangaren mu'amala da mutane.

Kara karanta wannan

Akwai dalili: Shekara 1 na Shugaba Tinubu ta fi shekaru 8 na mulkin Manjo Buhari, Reno Omokri

Wannan martani na ministan na zuwa ne yayin da 'yan kasar ke kokawa kan tsare-tsaren gwamnatin Tinubu da ta jefa al'umma cikin mawuyacin hali.

Tinubu ya fadi lokacin samun sauƙi

A baya, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin kawo sauki ga 'yan Najeriya nan da karshen shekarar da muke ciki.

Tinubu ya yi wannan alkawarin ne yayin da ake shan fama da tsadar rayuwa a fadin kasar baki daya.

Shugaban ya ce nan da watan Disambar wannan shekara da muke ciki komai zai daidaita a kasar kamar ba a yi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel