Kamfanin Karafa a Najeriya Ya Koka Kan Karancin Ma’aikata, Ya Ba Matasa Wata Dama

Kamfanin Karafa a Najeriya Ya Koka Kan Karancin Ma’aikata, Ya Ba Matasa Wata Dama

  • Wani kamfanin karafa mai suna Inner Galaxy da ke Owaza, jihar Abia ya koka kan karancin ma’aikata da yake fuskanta
  • Babban daraktan kamfanin, Lin Shanbiao ya ja hankalin matasa musamman jihar Abia da su nemi aiki a kamfanin
  • Shanbiao ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai wata ziyarar ban girma ga gwamnan jihar Abia, Alex Otti a Umuahia

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Umahia, jihar Abia - Babban daraktan kamfanin karafa na Inner Galaxy, Owaza, Lin Shanbiao, ya ce kamfanin na fuskantar karancin ma’aikata.

Kamfanin karafa na Inner Galaxy ya gana da gwamnan jihar Abia
Kamfanin Inner Galaxy ya yi kira ga matasa musamman jihar Abia da su nemi aiki a kamfanin. Hoto: @alexottiofr
Asali: Facebook

Mr. Lin Shanbiao ya ja hankalin matasa musamman jihar Abia da su nemi aiki a kamfanin la'akari da cewa kamfanin na a jiharsu, jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Kabir ya dauki zafi bayan sakin 'yan daba daga kulle, ya sha alwashi kan lamarin

Kamfanin karafa ya gana da Otti

Shanbiao ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci tawagar gudanarwar kamfanin zuwa wata ziyarar ban girma ga Gwamna Alex Otti a Umuahia, babban birnin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce, kamfanin wanda ya na aiki kan bangarori hudu, yana samar da rodi, hada sassan jikin tirela, samar da batirin mota, da sake sarrafa kwalabe.

"Mun zo nan ne domin tattauna wa da mai girma gwamna game da harkokin kasuwancinmu a jihar da kuma gano yadda za mu hada gwiwa ta hanyoyi da dama da gwamnati."

- In ji Shanbiao.

Gwamna Otti ya yi martani

Shafin BusinessDay ya rahoto Gwamna Otti ya ce yana da manufofi na jawo masu zuba hannun jari a jihar domin samar da ayyuka da inganta hanyoyin samun kudaden shiga.

"Wasu daga cikin manufofin da muka tsara sun shafi tallafawa masana'antun da ke aiki a yanzu da kuma jawo wasu sabbi zuwa jihar."

Kara karanta wannan

Akwai dalili: Shekara 1 na Shugaba Tinubu ta fi shekaru 8 na mulkin Manjo Buhari, Reno Omokri

- Alex Otti

Gwamnan ya kuma nemi kamfanin da ya gudanar da ayyuka masu inganci don jawo hankalin gwamnati tare da kawar samar da ingantaccen muhallin aiki.

Gwamna Radda ya yi sabon nadi

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Katsina, Malam Umar Dikko Radda ya nada Alhaji Falalu Bawale a matsayin sabon shugaban ma'aikata na jihar Katsina.

Alhaji Bawale ya karbi mukamin ne daga Alhaji Usman Isyaku wanda ya yi ritaya daga aikin gwamnati kuma aka nada shi mukamin mai ba Radda shawara kan harkokin gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel