NERC Ta Fayyace Wadanda Karin Kudin Wuta Ya Shafa, Ta Yi Karin Haske Kan Samun Wuta

NERC Ta Fayyace Wadanda Karin Kudin Wuta Ya Shafa, Ta Yi Karin Haske Kan Samun Wuta

  • Hukumar kula da wutar lantarki a Najeriya (NERC) ta bayyana yadda tsarin ba da wuta ke kasancewa a faɗin ƙasar
  • Hukumar ta fitar da jadawalin yadda ta ke rarraba wutar ganin yadda ake ta cece-kuce kan karin kudin wutar lantarki
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wata jami'ar hukumar wuta ta JED a Gombe kan wannan lamarin karin kudin wutar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Yayin da ake ta cece-kuce kan karin kudin wutar lantarki a Najeriya, an bayyana yadda gaskiyar abin ya ke.

A jiya Laraba 3 ga watan Afrilu ne Gwamnatin Tarayya ta sanar da karin kudin wutar a kasar.

Kara karanta wannan

Kano: Ganduje ya shiga sabuwar matsala yayin da Abba Gida-Gida ya dauki matakin bincike

Hukumar NERC ta fayyace yawan sa'o'i da ake samun wuta a Najeriya
Hukumar NERC ta fitar da jadawalin yawan sa'o'i da ake samun wuta a Najeriya. Hoto: Nigeria Electricity Regulatory Commission.
Asali: UGC

Karin kudin wuta ya jawo kace-nace

Hakan ya jawo ta da jijiyoyin wuya ganin yadda ba a samun wutar a wurare da dama a fadin kasar, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga bisani hukumar rarraba wutar a Najeriya ta yi karin haske kan wadanda karin kudin ya shafa.

Ta ce karin kudin ya shafi wadanda ke rukunin Band A da ke samun wutar akalla na sa'o'i 20 a kowace rana.

Kwastomomi da ke Band A sun samu karin kudin daga N66KwH zuwa N225KwH wanda su ne karin ya shafa.

Jerin yadda ake rarraba wuta a Najeriya

1. Rukunin Band A: su na samun wutar lantarki akalla sa'o'i 20 a kowace rana, kamar yadda NERC ta tabbatar a shafin Facebook.

2. Rukunin Band B: su na morar wutar lantarki akalla sa'o'i 16 a rana.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta cafke fitaccen ɗan daudu a Najeriya, Bobrisky a Legas

3. Rukunin Band C: Wannan rukuni na samun wutar lantarki akalla sa'o'i 12 a kowace rana.

4. Rukunin Band D: su ne wadanda ke samun wutar lantarki akalla sa'o'i takwas a kowace rana.

5. Rukunin Band E: su ne mafi karancin masu samun wuta akalla sa'o'i hudu a kowace rana.

Tattaunawar Legit Hausa da wasu kan lamarin

Legit Hausa ta ji ta bakin wata jami'ar hukumar wuta ta JED a Gombe kan wannan lamari

Khadijah Abdullahi ta ce tabbas karin ya shafi wadanda ke samun wuta da ya kai sa'o'i 20 a wuni.

Ta lissafo wasu unguwanni a Gombe da suke samun wuta sosai kamar Federal Low Coast da Jekadafari da Tumfure da sauransu.

Wani mazaunin Unguwar Gabukka, Ibrahim Yahaya ya tabbatar da cewa su na samun wuta fiye da sa'o'i 20.

'"Gaskiya wani lokaci muna samun wuta yafi wadannan sa'o'i da ake magana saboda da zarar ta dauke za ta dawo."

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fadi dalilin kara kudin wutar lantarki zuwa N225/KwH ga 'yan rukunin Band A

- Ibrahim Yahaya

Wani jami'in hukumar, Abba Mohammed ya ce Unguwanni kamar Jekadafari da Bolari da GRA da Tumfure su na samun wuta duk da cewa yanzu ya ragu sosai.

An kara kudin wutar lantarki

Kun ji cewa Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya, NERC ta tabbatar da kara kudin wutar lantarki a Najeriya.

Mataimakin shugaban NERC, Musliu Oseni shi ya bayyana haka ga manema labarai inda ya ce an kara kudin daga N66/KwH zuwa N225/KwH.

Asali: Legit.ng

Online view pixel