'Yan Bindiga da Masu Daukar Nauyinsu Sun Shiga Uku, An Ji Abin da Zai Faru da Su a Najeriya
- Fitaccen limamin coci, Bishof David Oyedepo ya ce nan da yan kwanaki 'yan bindiga da masu daukar nauyinsu za su gamu da hukuncin Ubangiji
- Oyedepo ya bayyana cewa duk mai hannu a kashe rayukan bayin Allah ko garkuwa da mutane zai girbi abin da ya shuka a kasar nan
- Wannan kalamai na zuwa mlne bayan gwamnatin tarayya ta saki sunayen wasu mutane da take zargi da daukar nauyin ta'addanci a Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ogun, Nigeria - Jagoran cocin Living Faith Church Worldwide, Bishof David Oyedepo ya hango abin da zai samu 'yan bindiga da masu daukar nauyinsu nan ba da jimawa ba a Najeriya.
Fitaccen malamin addinin kirista ya yi addu'o'i a ranar Lahadi, 19 ga watan Afrilun 2025, tare da neman hukuncin Ubangiji ya tabbata a kan ‘yan bindiga da masu daukar nauyinsu a fadin kasar nan.

Source: Twitter
Oyedepo ya tabo batun 'yan bindiga
Tribune Nigeria ta rahoto cewa Bishof Oyedepo ya bayyana hakan ne yayin wani taron ibada mai taken “Ranar Alkawarin Ramuwar Gayya” da aka gudanar a hedkwatar cocin da ke Ota, jihar Ogun.
Limamin cocin ya ce duk wadanda ke da hannu a kashe-kashen ta'addanci, da sace mutane da niyyar neman kudin fansa, za su fuskanci sakamako cikin kankanin lokaci.
“Ina ayyana hukunci a kan duk wadanda suka haddasa wadannan masifu da kuma masu goyon bayansu da sunan Yesu,” in ji shi.
Malamin ya kara da cewa ramuwar Ubangiji za ta tabbata cikin gaggawa, yana mai jaddada cewa hakan ba zai dauki lokaci mai tsawo ba.
“Sai dai idan ba wahayi aka mani ba, amma wannan abu zai faru cikin kwanaki bakwai masu zuwa,” in ji Oyedepo.
"Allah zai kawo dauki Najeriya" - Oyedepo
Oyedepo ya kuma nuna kwarin gwiwa cewa nan gaba kadan ‘yan Najeriya za su fara ganin sakamakon abin da ya kira daukin Allah cikin lamarin, inda ya ce kwanaki masu zuwa za su zo da “shaida ta ramuwar gayya.”
Wannan wahayi da malamin cocin ya yi ikirarin an masa na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar tsaro ke kara tabarbarewa, inda yan ta'adda ke kai hare-hare kan sansanonin sojoji da fararen hula.

Source: Instagram
A makonnin da suka gabata Gwamnatin tarayya ta ayyana sunayen wadanda take zargi da daukar nauyin 'yan bindiga a sassan kasar nan, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Sai dai Bishof Oyedepo ya ce da yan bindiga da duk masu daukar nauyinsu, za su gamu da fushin Allah cikin kwanaki bakwai masu zuwa, inda ya ce yan Najeriya za du ga sauyi kwanan nan.
An hukunta yan ta'adda 386 a Najeriya
A baya, kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta kammala shari'ar mutane 508 da ake zargi da ta'addanci, inda aka samu nasarar yanke wa mutane 386 hukunci.
Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi, ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan kammala kashi na tara na shari’ar 'yan ta'addar da aka gudanar a cikin mako guda.
A cewar ministan, daga cikin mutane 508 da aka kawo gaban kotun, mutane takwas aka sallama, yayin da aka wanke mutane biyu baki ɗaya.
Asali: Legit.ng

