An Shiga Fargaba Bayan Wata Ta Watsawa Fitacciyar Mawakiyar Najeriya Ruwan Batir

An Shiga Fargaba Bayan Wata Ta Watsawa Fitacciyar Mawakiyar Najeriya Ruwan Batir

  • Wata fitacciyar mawakiya ‘yar Najeriya ta gamu da wani iftila’i bayan watsa mata ruwan batir da kuma kai mata farmaki da wuka
  • Mawakiyar wacce kuma ta kware wurin yin rawa mai suna Korra Obidi ya gamu da tsautsayin ne a yayin da ke tsaka da rawa a Landan
  • A cikin wani faifan bidiyo da ta wallafa a shafinta na Instagram, Obidi ta bukaci taimakon jama’a wurin zakulo wacce ta aikata hakan

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Landan, Burtaniya – Fitacciyar mawakiya kuma ’yar rawa ta gamu da tsautsayi bayan an watsa mata ruwan batir a jiki.

Mawakiyar wacce ‘yar Najeriya ce mai suna Korra Obidi ta gamu da tsautsayin ne yayin da ta ke tsaka da rawa a Burtaniya.

Kara karanta wannan

Mun dauki matakan saukar da farashin gas, cewar ministan mai

An watsawa mawakiyar Najeriya ruwan batir ta na tsaka da wasa
Mawakiya, Korra Obidi ta gamu da tsautsayi bayan wata ta watsa mata ruwan batir a Burtaniya. Hoto: @korraobidi.
Asali: Instagram

Mawakiyar ta bayyana surar wacce ake zargi

Obidi ta wallafa faifan bidiyo a shafinta na Instagram a jiya Alhamis 11 ga watan Afrilu inda ta ce matashiyar ta kuma kai mata farmaki da wuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mawakiyar wacce bazawara ce mai ‘ya’ya biyu ta ce wacce ta kai mata harin baka ce kuma mai tsayi.

“A yanzu haka muna cikin motar marasa lafiya domin zuwa asibiti, an kai mani farmaki da wuka da kuma ruwan batir a Burtaniya lokacin da na ke wasa.”
“Akwai yawan matsaloli da tsana a baya amma wannan abin da ya faru na cin zarafi ne a zahiri ya kamata mu farka.”
“Idan kuna da wani bayani game da wacce ta kawo harin, mace ce baka mai tsayi, ku taimaka a tura ta wannan adireshin Korramanagement@gmail.com.”

- Korra Obidi

Matakin da mawakiyar ta dauka

Kara karanta wannan

"Ya ki ya sumbace ta": Ango ya kunyatar da amaryarsa a gaban jama'a a wajen daurin aure

Mawakiyar ta bayyana yadda ta ke cikin tsananin ciwo inda ta bukaci lemon kalba na “Coke” domin ta wanke jikinta.

Ta dauki matakin wanke jikin nata ne da lemon kwalbar bayan tabbatar da cewa zai rage radadin zafin gubar da aka watsa mata.

Wasu jami’an tsaro sun samu isowa inda lamarin ya faru inda suka taimaka mata wurin zuba lemon kwalbar a jikinta.

Wani ya watsawa mutane ruwan batir

A wani labarin, wani mutum ya watsawa mutane takwas ruwan batir a wata kasuwa da ke jihar Anambra a Najeriya.

Lamarin ya faru ne bayan wata ‘yar sabani ta shiga tsakanin mutanen inda tuni wanda ake zargin ya tsere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel