NAPTIP Ta Cafke ‘Malamar Addinin Kirista’ da Zargin Sato Wasu Kananan Yara 38

NAPTIP Ta Cafke ‘Malamar Addinin Kirista’ da Zargin Sato Wasu Kananan Yara 38

  • Jami’an NAPTIP sun yi nasarar kama wata mata wanda aka samu da kananan yara rututu da ake zargin sato su aka yi
  • Wadannan yara sun koma hannun marikansu yayin da NAPTIP take bakin kokari wajen hana yin safarar mutane Najeriya
  • Shugaban hukumar NAPTIP na sashen Benin, Nduka Nwanwene ya ce sunan matar da aka kama Ikejimba Maryvianney

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Delta - Hukumar NAPTIP ta kama wata mata mai suna Ikejimba Maryvianney da zargin satar wasu kananan yara a jihar Delta.

Jami’an NAPTIP na shiyyar Benin sun damke wannan mata mai shekaru 40 kuma sun mika yaran da aka samu gaban iyayensu.

NAPTIP
NAPTIP ta ceto yara 38 da aka sace a Delta Hoto: Getty Images (An yi amfani da hoton nan domin misali ne)
Asali: Getty Images

NAPTIP ta mika yara ga iyayensu

Jaridar Daily Trust ta ce an kai yaran wajen iyayen nasu ne a sansanin Enugu-Awka da ke garin Monastery, Ilah, a jihar Delta.

Kara karanta wannan

Dala a babbar riga: Hadimin Atiku ya dage, yana so hukumar EFCC ta binciki Ganduje

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban NAPTIP na sashen Benin, Barista Nduka Nwanwene ya tabbatar da cafke wannan mata da ya zanta da ‘yan jarida.

Barista Nduka Nwanwene ya ce wannan mata tana karyar ita limamiyar coci ce, ba yau aka saba samun labari irin haka ba.

Yadda Ikejimba Maryvianney ta sace yara 38

Kamar yadda PM News ta kawo rahoto, wata mai suna Chidera ce ta taimakawa Ikejimba Maryvianney wajen satar yaran.

Madam Ikejimba Maryvianney ta sulale da su ne da sunan za ta kula da su fiye da irin kulawar da suke samu a gidan marayu.

A lokacin da ta dawo yankin domin sake daukar wasu yaran, a nan aka ankarar da jami’an NAPTIP wadanda suka cafke da ita.

Malamar addini da satar kananan yara?

Sahara Reporters ta ce Nwanwene ya nuna wanda ake zargi ta yi ikirarin ta samu horaswar addinin kiristanci a kasar Ghana.

Kara karanta wannan

Taushen Fage: Al'adar cin nama da sada zumunta da ta shekara sama da 100 a Sakwaya

A cewar Maryvianney, hedikwatarsu ta addini ta na kasar Philippines. NAPTIP mai yaki da safarar mutane ba ta yarda da ikirarin ba.

Ana zargin matar tayi suna wajen sace yara a garin Owerri da kewaye, daga nan sai ta sallama su ga wadanda za sui ya safararsu.

Najeriya na cikin barazanar kudi

Idan aka yi rashin sa'a, danyen man kasar nan za su iya yin kwantai a kasuwannin duniya kamar yadda aka ji a wani rahotonmu.

Jiragen da aka fita da su suna jibge ba tare da an samu mai saye ba saboda gyaren manyan matatu da yajin-aiki a kasashen Turai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel