Kano: An Shiga Fargaba Yayin da Gungun Matasa Suka Hallaka Wani Almajiri Ɗan Shekaru 16

Kano: An Shiga Fargaba Yayin da Gungun Matasa Suka Hallaka Wani Almajiri Ɗan Shekaru 16

  • An shiga wani irin yanayi bayan wasu matasa sun hallaka wani almajiri mai shekaru 16 kan zargin kisan wani yaro
  • Matasan sun dauki matakin ne bayan zargin almajirin ya guntule kan yaro mai suna Mohammed Sa'idu
  • Lamarin da ke cike da takaici ya faru ne a kauyen Kanwa da ke karamar hukumar Madobi a jihar Kano

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Wasu fusatattun matasa sun yi ajalin wani almajiri kan zargin guntuke kan wani yaro mai shekaru shida a jihar Kano.

Almajirin mai shekaru 17 da ake kira Abdullahi ya gamu da tsautsayin ne bayan zargin kisan yaron mai suna Mohammed Sa'idu.

Kara karanta wannan

Yayin da ya fara fitar da mai, Dangote ya samo mafita kan tsadar kayayyaki a Najeriya

Fusatattun matasa sun hallaka wani almajiri a Kano
Wasu matasa sun yi ajalin almajiri a Kano kan zargin guntule kan yaro. Hoto: @KanoPoliceNG.
Asali: Twitter

A wani kauye lamarin ya faru a Kano?

Lamarin ya faru ne a kauyen Kanwa da ke karamar hukumar Madobi a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan 'yan sanda a jihar, Mohammed Hussaini Gumel shi ya tabbatar da haka ga manema labarai a yau Juma'a 12 ga watan Afrilu.

Gumel ya ce an tsinci gawar yaron ba tare da kai ba a gefen makarantar Firamare da ke kauyen bayan dogon bincike.

Ya ce an dauki gawar zuwa asibiti domin yin gwaji kafin daga bisani a mika ta ga 'yan uwansa domin mata sutura, cewar Vanguard.

Ya kara da cewa wanda ake zargin ya tabbatar da aikata laifin inda ya ce ya jefar da kan ne a cikin shaddar da ke kusa da makarantar.

Yadda lamarin ya faru a Kano

Kara karanta wannan

Wuraren shakatawa 5 da ya kamata ku ziyarta yayin bukukuwan Sallah a Kaduna

Dagacin kauyen, Umar Maitama Yusuf ya ce wanda ake zargin ya taba aiki a gidansu marigayin kafin a kore shi kan zargin sata.

Yusuf ya ce fiye da mutane 10,000 ne suka fi karfin 'yan sanda da jami'an NSCDC a fadarsa inda suka zakulo yaron.

"Sun lalata wani bangare na fadar a kokarin kashe yaron, wasu sun haura ta saman kwano domin dauko yaron yayin da suka gagara bude kofar."
"Daga bisani sun gano dakin da ya ke suka hallaka shi saboda sun yi tunanin idan suka mikawa 'yan sanda za a sake shi daga baya."

- Umar Maitama

An gano shirin birkita Kano

Kun ji cewa rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta gano wani shiri na kawo rudani a fadin jihar baki daya.

Rundunar ta ce ta na zargin wasu kungiyoyin addini da na siyasa kan kokarin kawo rashin tsaro yayin bukukuwan sallah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel