Karfin Hali: Uba da Dansa Sun Yi Taron Dangi, Sun Yiwa Matar Makwabcinsu Duban Mutuwa a Ogun

Karfin Hali: Uba da Dansa Sun Yi Taron Dangi, Sun Yiwa Matar Makwabcinsu Duban Mutuwa a Ogun

  • 'Yan sanda sun kama uba da dansa bisa zarginsu da kashe wata mata kan musayar miyau da ta faru tsakaninsu
  • Rahoto ya bayyana yadda lamarin ya faru da kuma yadda aka kai ga kame mutanen biyu da ke zaune gida daya
  • Ya zuwa yanzu, 'yan sanda na ci gaba da bincike kan yadda za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Ogun - Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta ce jami’anta sun cafke wani mutum mai suna Chizoke Obiadada mai shekaru 54 da kuma dansa mai shekaru 17 mai suna Micheal bisa laifin kashe matar makwabcin su, Tope Owoade.

Kara karanta wannan

Kisan 'Yan Sanda a Delta: An kame mutum da ake zargi da yiwa jami'ai kisan gilla

An ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 28 ga Maris, 2024 a Ogijo da ke karamar hukumar Sagamu ta jihar ta Ogun.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Omolola Odutola, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar 30 ga watan Maris.

An kama uba da dansa kan laifin kisa
Uba da dansa sun kashe wata mata a Ogun | Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta yaya lamarin ya kai ga kashe matar makwabci?

An ce Obiadada da dansa sun yi artabu da marigayiyar ne bayan barkewar musayar miyau a tsakaninsu kan teburin da take siyar da fatar shanu, wanda aka fi sani da “ponmo”.

An kama wadanda ake zargin ne bayan mijin mamacin, Isiaka, ya kai rahoton aukuwar lamarin ga ‘yan sanda a hedikwatar shiyya ta Ogijo, rahoton jaridar Guardian.

Bayan samun wannan rahoton ne babban jami’in yankin ya ba da umarnin a kamo wadanda suka aikata laifin, kuma a halin yanzu suna gudanar da bincike a matakin farko.

Kara karanta wannan

Rikicin Jihar Plateau: Fulani na zargin sojojin Najeriya da yi masu bakin aika-aikata

Matakin da za a fara dauka a yanzu

Odutola ya ce za a mayar da shari’ar zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar domin gudanar da bincike mai zurfi.

A halin da ake ciki, ba a samu jin ta asibitin da aka kwantar da matar ba don jin rahoton binciken gawarta, Daily Post ta ruwaito.

Ba wannan ne karon farko da ake samun irin wannan kitimurmura ba a jihohin Najeriya, hakan ya sha faruwa a lokuta mabambanta.

Wani ya kashe diyar makwabcinsa

A wani labarin kuma, jami'an tsaro sun damke wani mutumi mai suna Kabiru Abdullahi wanda ake zargi da kisan diyar makwabcinsa, Khadija yar shekara biyar a jihar Bauchi.

Kakakin hukumar Civil Defence na jihar, Garkuwa Adamu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Litinin, rahoton ChannelsTV.

Ya yi bayanin cewa an damke Abdullahi ne tare da Alhaji Yawale kan zargin garkuwa da diyar Abdullahi Yusuf a Sabon Gari Narabi a karamar hukumar Toro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel