Fusatattun Fasinjoji Sun Yi Wa Jami'in Tsaro Kisan Gilla a Katsina, Bayanai Sun Fito

Fusatattun Fasinjoji Sun Yi Wa Jami'in Tsaro Kisan Gilla a Katsina, Bayanai Sun Fito

  • An shiga wani irin yanayi bayan wasu fasinjoji sun hallaka jami'in hukumar Kwastam a jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya
  • Fasinjojin sun dauki matakin ne bayan jami'in ya bindige wani fasinja a karamar hukumar Kaita da ke jihar
  • Tahir Balarabe, kakakin hukumar a Katsina ya tabbatar da haka inda ya ce hukumar za ta fitar da sanarwa kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Wasu fasinjojin manyan mota sun hallaka jami'in hukumar Kwastam a jihar Katsina.

Mutanen sun dauki wannan mummunan matakin ne bayan jami'in hukumar ya harbe wani fasinja.

Wasu fasinjoji sun hallaka jami'in tsaro a Katsina
An hallaka jami'in hukumar Kwastam bayan harbin fasinja a jihar Katsina. Hoto: @CustomsNG.
Asali: Twitter

Yaushe aka yi ajalin jami'in tsaron?

Lamarin ya faru ne a yau Laraba 17 ga watan Afrilu a kan hanyar Katsina zuwa Dankama a karamar hukumar Kaita da ke jihar.

Kara karanta wannan

Sojoji sun bindige 'yan sakai da fararen hula yayin harin Filato? Gaskiya ta fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta tattaro cewa direban ya dauko fasinja zuwa Dankama yayin da wani jami'i ya yi kokarin tsayar da shi amma yaƙi tsayawa.

Wanan ya sa wani jami'in hukumar ya ciro bindiga tare da harbin fasinjan a ƙugu.

Daga bisani direban ya tsaya inda fasinjan suka durfafi jami'an domin daukar fansa, cewar rahoton Tori News.

Fasinjojin sun hallaka jami'in hukumar nan take bayan kisan fasinjan da ya yi mai suna Bashir Na-Buzuwa.

Martanin hukumar kan faruwar lamarin

Na-Buzuwa mai shekaru 27 ya fito ne daga kauyen Doro da ke karamar hukumar Bindawa sai dai mazaunin Zanguna ne a Katsina.

Kakakin hukumar Kwastam a Katsina, Tahir Balarabe ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce za su fitar da sanarwa daga baya.

Balarabe ya ce a yanzu haka hukumar na kokarin daukar gawan jami'in nasu da aka hallaka ne yayin hatsaniyar.

Kara karanta wannan

Iftila'i: Mummunar gobara ta shafe kasuwar Boda dake Gaya

'Yan bindiga sun farmaki rumbun abinci

A baya, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari kan rumbun abincin Gwamnatin Tarayya a jihar Katsina.

Maharan sun kai farmakin ne a karamar hukumar Dutsinma wanda jami'an tsaron hukumar NSCDC suka dakile harin.

Wannan na zuwa yayin da ake yawan samun fasa rumbunan abinci a fadin kasar saboda halin yunwa da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel