An Yi Babban Rashi a Fadar Masarautar Nupe, Gwamna Bago Ya Yi Ta'aziyya
- An wayi gari da rasuwar Son Fada na Etsu Nupe, Mahmud Abubakar a jihar Neja bayan shafe shekaru yana hidima wa al'ummar yankinsa
- Gwamna Umaru Bago ya fitar da sakon ta'aziyya, inda ya bayyana rasuwar basarake a matsayin babban rashi ga al'ummar jihar Neja
- Umaru Bago ya kuma ambaci gudunmuwar marigayin wajen kawo zaman lafiya da cigaba a jihar Neja da kasa baki daya a lokacinsa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Neja - Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, ya mika sakon ta’aziyyar rasuwar babban jami'i a masarautar jihar ga mai martaba Etsu Nupe, Yahaya Abubakar.
Gwamna ya yi ta'aziyya ga masarautar Nupe da kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta jihar Neja, bisa rasuwar Mahmud Abubakar da ke rike da sarautar Son Fada.

Source: Facebook
A cikin sakon ta’aziyyar da hadimin gwamnan, Bologi Ibrahim, ya fitar a Facebook, Bago ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ba ga masarautar Nupe kadai ba har ma da daukacin jihar.
Sakon ta'aziyyar Gwamna Umaru Bago
Gwamna Bago ya mika ta’aziyyarsa ga masarautar Bida da iyalan mamacin, inda ya roki Allah ya gafartawa Son Fada na masarautar Nupe kura-kuran shi tare da rokon Allah ya sanya shi a Aljannar Firdausi.
Leadership ta wallafa cewa gwamnan ya ce za a cigaba da tunawa da gudunmuwar da ya ba al'ummar jihar da kasa baki daya a lokacin rayuwarsa.
Sakon Bago ga iyalan mamacin
Bago ya bukaci iyalan su ci gaba da jajircewa wajen yi wa marigayin addu’a tare da koyi da kyawawan ayyukansa na hidimtawa al’umma.
Sanarwar gwamnatin Neja ta ce:
“Ya yi addu’ar cewa iyalan marigayin Alhaji Mahmud za su ci gaba da jajircewa wajen yi masa addu’a tare da koyi da kyawawan ayyukansa na hidimtawa al’umma,”
Gwamnan ya tuna da muhimmiyar gudunmawar da marigayi Sonfada ya bayar wajen ci gaban masarautar Nupe da jihar Neja baki daya.
Sanarwar ta kara da cewa:
“Gwamnan ya tuna da dimbin gudunmawar da marigayi Sonfada ya bayar wajen ci gaban masarautar Nupe da jihar gaba daya, yana mai cewa za a ci gaba da tunawa da su tare da ambato su a tsawon shekaru masu zuwa.”

Source: Facebook
Biyo bayan haka, al'umma da dama sun yi addu'o'i ga marigayin a kafafen sada zumunta suna rokon Allah ya gafarta masa kurakuran da ya aikata a baya.
Rahotanni sun nuna cewa an riga an yi wa margayi Son Fada Etsu Nupe, Mahmud Abubakar jana'iza tare da birne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Ana maganar tsige Sarkin Ibadan
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose ya yi zargin cewa Gwamnatin jihar Oyo ta fara shirin tsige Sarkin Ibadan.
Fayose ya sanar da cewa a kwanakin baya ya yi zargin aikata hakan amma aka karyata shi, inda ya ce a yanzu ya kara samun hujjoji masu yawa.
Gwamnatin jihar Oyo da masarautar Ibadan sun fito sun karyata ikirarin tsohon gwamnan, inda suka ce babu kamshin gaskiya a cikin kalamansa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

