Zanga-Zanga Ta Ɓarke Yayin da Sojoji Suka Kashe Bayin Allah da dama a Arewacin Najeriya

Zanga-Zanga Ta Ɓarke Yayin da Sojoji Suka Kashe Bayin Allah da dama a Arewacin Najeriya

  • Zanga-zanga ta ɓarke a Gashua da ke jihar Yobe yayin da ake zargin dakarun sojoji sun kashe mutane akalla 4 a shingen bincike
  • Ganau ya bayyana cewa sojojin sun buɗe wa mutane wuta a shingen binciken su da ke Tashan Kuka, lamarin da ya fusata mazauna yankin
  • Wani jami'in tsaro ya tabbatar da cewa mutum huɗu ne suka mutu yayin da wasu dama da 10 suka samu raunuka daban-daban

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Yobe - Mazauna garin Gashua a jihar Yobe sun yi zanga-zangar nuna rashin jin daɗinsu bisa zargin dakarun sojojin Najeriya da kashe mutum huɗu.

Masu zanga-zangar sun zargi sojojin da aka turo su kare rayukan al'umma da kashe mai adaidaita sahu guda ɗaya da kuma wasu mutum uku a Gashua.

Kara karanta wannan

Ke duniya: An kama wani mutum da zargin kashe mahaifiyarsa mai shekaru 100 a Najeriya

Sojojin Najeriya.
Ana zargin sojoji sun kashe mutane a Yobe Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta tattaro cewa cewa mutanen sun yi zanga-zangar cikin lumana a kan tituna, sun kuma nuna ɓacin rai kan lamarin wanda ya faru bayan sojoji sun buɗe wuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya faru ne jiya a daya daga cikin shingayen binciken sojoji da ke Tashan Kuka a kan titin Garin Alkali ta Gashua, hedikwatar karamar hukumar Bade a jihar Yobe.

Meyasa sojoji suka kashe mutane?

An gano cewa wasu sojoji sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi yayin da daruruwan masu zanga-zangar suka tunkari shingen bincikensu da ke Tashan Kuka.

Yayin haka ne suka yi ajalin mai keke Napep ɗin, wanda hakan ya haddasa sabuwar zanga-zanga, rahoton Arise TV.

Daya daga cikin masu zanga-zangar, Adamu Bukar, wanda ya yi magana da yarensa, ya ce:

"Ba zamu yarda da kashe mana ƴan uwanmu ba, bama son sojoji su ci gaba da zama a Gashua.

Kara karanta wannan

Kano: An shiga fargaba yayin da gungun matasa suka hallaka wani almajiri ɗan shekaru 16

Adadin mutanen da suka mutu

Wata majiya ta daban ta ce sojojin sun kashe mutum biyar yayin arangamar sannan sun jikkata wasu 14 kuma tuni aka garzaya da su asibitin kwararru na Gashua domin yi musu magani.

A cewar Hassan Bala, wanda ya yi ikirarin cewa a gabansa aka yi, zuwan sojojin kwatsam ya haifar da firgici a tsakanin mutanen da ke shingen binciken Tashan Kuka.

Wani jami’in tsaro a yankin ya tabbatarwa jaridar ta wayar tarho cewa mutane hudu ne suka mutu sannan 13 sun samu raunuka daban-daban.

Zanga-zanga a kauyen Zamfara

A wani rahoton kuma mazauna ƙauyen Kukawa a karamar hukumar Maradun a Zamfara sun yi ikirarin sojoji sun masu ruwan bama-bamai a filin idi ranar Laraba.

Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya ce jirgin ya zo wucewa sai ƴan bindiga suka buɗe masa wuta bisa haka ya saki bam ɗin da ya shafi fararen hula.

Asali: Legit.ng

Online view pixel